Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-08 14:45:28    
Jama'ar Afrika na nuna himma ga saye da sayar da takardun hada-hadar kudi

cri

A sakamakon kara gudanar da harkokin siyasa a yawancin kasashen Afrika kamar yadda ya kamata, kasuwannin kasashen nan ma suna ci sosai. A cikin shekarun nan da suka wuce, kasashen Afrika da ke kudancin Sahara kamar Kenya da Nijeriya da Tanzaniya da Uganda da Zambiya da sauransu sun bunkasa harkokin tattalin arzikinsu yadda ya kamata, sa'an nan kuma kasuwannin hada-hadar kudinsu ma kullum sai kara ci suke yi.

Bisa wani rahoton da bankin binciken adadin kudi na Afrika ya bayar a shekarar bara, farashin hannun jari na kasuwannin hada-hadar kudi na Afrika ban da na kasar Afrika ta kudu ya karu da kashi 56 cikin dari a shekarar 2005, wato ke nan ya wuce na nahiyoyin Asiya da Turai da kuma Amurka ta arewa da ta kudu, har ma ya kai matsayin farko a duk duniya.

Daga adadin da aka bayar, an gano cewa, farashin hannun jari na kasuwar hada-hadar kudi ta kasar Masar ya karu da kashi 155 cikin dari a shekarar 2005. Saurin hauhawar farashin nan ya kai matsayin farko a duk duniya a waccan shekarar. Babban dalilin da ya sa haka, shi ne domin kasar Masar ta kara jawo masu zuba jari a kasuwar hada-hadar kudi ta hanyar yin kwaskwarima kan harkokin tattalin arziki da kara samun kudin shiga daga man fetur.

Haka kuma farashin hannun jari na kasuwar hada-hadar kudi ta kasar Zambiya ma ya karu da kashi 116 cikin dari a shekarar 2005, saurin karuwar farashin nan ya kai matsayi na biyu a duniya. Haka kuma irin wannan farashi ya tashi sosai a kasuwannin hada-hadar kudi na kasashen Morocco da Botswana da Kenya da kuma sauran kasashe.

Babban dalilin da ya sa kasuwannin hada-hadar kudi na Afrika ke ci sosai, shi ne domin ci gaban da aka samu wajen bunkasa harkokin tattalin arziki da kwaskwarima da aka yi kan harkokin siyasa a nahiyar. Yanzu, matsakaicin kudin da ko wane mutumin Afrika ke samu daga wajen samar da kayayyaki wato GDP ya kai wani sabon matsayi da ba a taba ganin irinsa ba a cikin shekaru sama da 10 da suka wuce.

Kasar Kenya na daya daga cikin kasashen Afrika da ke nuna himma ga saye da sayar da takardun hada-hadar kudi. A shekarar 2006, manyan kamfanonin gwamnatin kasar Kenya hudu sun sayar da hannun jari a kasuwar hada-hadar kudi. Hannun jarin da suka sayar sun sami karbuwa sosai daga wajen masu zuba jari. Ministan kudi na kasar Kenya ya taba bayyana cewa, gwamnatin kasar ta mayar da wadannan kamfanoni zama kamfanoni masu zaman kansu, makasudinta shi ne don kara kula da kamfanonin da kyau.

An kafa kasuwar hada-hadar kudi ta Nairobi a shekarar 1954. Tun bayan da Mwai Kibaki ya hau karagar mulkin kasar a shekarar 2002, sai ya fara yin kwaskwarima kan harkokin tattalin arziki, ta haka an bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar cikin sauri. Yanzu, saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar ya kan kai kashi 6 cikin dari a kowace shekara. Sakamakon haka, kasuwar hada-hadar kudi ta Nairobi ta fara ci sosai.

Bisa taimakon gwamnatin kasar, an mayar da kasuwar hada-hadar kudi ta Nairobi irin ta kulob din masu hannu da shuni da ta zama ta jama'a. Wani jami'in kasuwar hada-hadar kudi ta Nairobi ya bayyana cewa, 'yanzu kwararru da tsofaffi masu ritaya daga aiki da manoma da samari da kuma dalibai gaba daya suna nuna himma ga saye da sayar da takardun hada-hadar kudi a kasar.'

Al'ummar kasar Kenya ta sami manyan sauye-sauye ta hanyar cin kasuwar hada-hadar kudi. A da, shanu da filaye ma'auni ne ga dukiyoyin jama'ar kasar Kenya, amma yanzu ba haka ba ne wato takardun hada-hadar kudi sun zama ma'auni ga bunkasuwar dukiyoyin jama'ar.

A sakamakon karuwar kudin shiga da suke samu, jama'ar kasar Kenya suna sha'awar yin yawon shakatawa a kasashen ketare. Salula da katunan banki da yawon shakatawa a birnin Paris manyan abubuwa uku ne da ake nunawa a kan allunan talla da aka kafa a titunan birnin Nairobi. Dakunan cin abinci da otel-otel ma kullum sai kara ci suke yi, inda samari su kan yi nishadi a daren ko wace rana. (Halilu)