A halin yanzu, ana nan ana mashashan aiki wajen gina dakuna da kuma filayen wasan motsa jiki na Olympics da kuma kyautata muhallin birnin Beijing; Ban da wannan kuma, ana namijin kokari wajen gwada kyakkyawar fuskar Beijing, da yadada al'adun kasar Sin da kuma yin farfaganda kan hasashen Olympics. A kwanakin baya ba da dadewa ba, kwamitin shirya taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing ya gayyaci Sinawa taurari da yawansu ya wuce 100 daga da'irorin nishadi da na wasannin motsa jik don su gudanar da jerin harkokin nuna wasannin fasaha da na motsa jiki, ta yadda za a kara habaka kyakkyawan tasirin da taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing zai janyo.
Ayyukan share fage ga taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing a shekarar 2008 sun samu cikakken goyon baya daga wajen gwamnatin kasar Sin da jama'arta, haka kuma sun fi jawo hankulan kasashen duniya. Bisa shirin da kwamitin shirya taron wasannin Olympics na Beijing ya tsara,an ce yayin da ake daukaka ci gaban aikin gina dakuna da kuma filayen wasannin motsa jiki na Olympics da kuma na kyautata muhallin birnin Beijing, kamata ya yi a ingiza yunkurin yin farfaganda kan hasashen taron wasannin Olympics na " zamantakewar al'adu". Lallai ana bukatar jama'a da su nuna himma da kwazo wajen shiga harkoki iri daban daban dake shafar hasashen ' zamantakewar al'adu'. Domin tada sha'awar mutane ga shiga harkokin da kuma habaka tasirin taron wasannin Olympics na Beijing, kwamitin shirya taron wasannin Olympics na Beijing na kokarin yin amfani da ' sakamako mai amfani da mutane taurari da suka shahara' za su haddasa. Hakakuma an kafa wata ' kungiyar sa kaimi ta Sinawa taurari' ta kafu, wadda take kunshe da shahararrun 'yan wasan fasaha da kuma wassu mutane taurari daga da'irar wasannin motsa jiki da yawansu ya wuce 100, wadanda suka zo daga babban yankin kasar Sin da kuma yankin Hongkong, da na Macao da kuma na Taiwan.Manufarsu ita ce, yin amfani da karfin kira da suke da shi don gwada kyakkyawar fuskar Beijing, da yadada al'adun kasar Sin da kuma yin farfaganda kan hasashen wasannin Olympics.
Mr. Yu Zaiqing, mamban zartarwa na kwamitin wasannin motsa jiki na Olympics na kasa da kasa kuma mataimakin shugaban kwamitin shirya taron wasannin Olymiics na Beijng ya yi hasashen, cewa
'Gayyatar wassu mutane taurari daga da'irorin nishadi da na wasan motsa jiki ga habaka kyakkyawan tasirin da taron wasannin Olympics na Beijing zai janyo, wani babban abun kagowa ne. Ko shakka babu za a iya samun sakamako mafi kyau. A ganina, shiga cikin wannan kungiyar sa kaimi ta Sinawa taurari da ' yan wasan fasaha daga yankin Hongkong da Macao da kuma na Taiwan suka yi, labuddah zai yi babban tasiri ga dukkan Sinawa mazauna kasashen ketare.
Shahararren dan wasan fasaha mai suna Zeng Zhiwei daga yankin Hongkong ya yi farin ciki da fadin, cewa: ' Lallai za mu yi fama da aiki nan da shekaru biyu masu zuwa. Za a gudanar da harkar farfaganda kusan a kowane wata. Bari mu yi karbe-karben aiki, wato idan wani yana da lokaci, sai ya shiga harkar. A nan ina kira ga baki daga ketare da su zo nan Beijing don duba yadda jama'ar kasar Sin suke yin aiki da kyau wajen shirya taron wasannin motsa jiki na Olympics'.
A nan gaba, wannan kungiyar sa kaimi za ta taimaki kwamitin shirya taron wasannin Olympics na Beijing wajen yin farfaganda iri daban daban domin jama'a; Ban da wannan kuma, za ta shiga harkar farfaganda kan al'adu, da wasannin motsa jiki, da aikin kiyaye muhalli da kuma wasan bai wa juna wutar yula domin taron wasannin Olympics na Beijing.
Wadannan 'yan fasaha taurari sun jaddada, cewa taron wasannin Olympics na Beijing a shekarar 2008, wani babban lamari ne na dukkan jama'ar kasar Sin. Wata sannanniyar mawakiya mai suna Cheng Fangyuan ta babban yankin kasar Sin ta rera wata wakar dake bayyana kirarin taron wasannin Olympics. Wakar nan tana da lakabin haka: ' Duniya daya, kuma buri daya'. Mawakiya Cheng Fangyuan ta furta, cewa ' An kafa wannan kungiyar sa kaimi ne domin jawo hankulan mutane da su zura ido kan taron wasannin Olympics. Mu kam a matsayin mashahuran mawaka, za mu ba da taimako gwargwadon iyawa ga wannan gagarumin taro'.
|