A ran 2 ga wata, bangaren sojan kasar Amurka ya bayar da wata sanarwa cewa, an rigaya an kafa hedkwatar bada umurni ta Afrika ta sojojin kasar Amurka a hukumance, wadda ta fara aiki a ran 1 ga wata. Nauyin dake bisa wuyanta shi ne daidaita harkokin tsaro na kasashen Afrika da na yaki da ta'addanci. Sanarwar ta ce, a shekara ta farko dai, hedkwatar bada umurni ta Afrika za ta yi aiki a birnin Stuttgart na kasar Jamus,ne inda ya kasance da sansanin hedkwatar bada umurni ta sojojin kasar Amurka a Turai har zuwa watan Oktoba na shekara mai kamawa.
A ran 6 ga watan Fabrairu na shekarar da muke ciki, shugaba Bush na kasar Amurka ya amince da kafa hedkwatar bada umurni ta sojojin kasar Amurka a Afrika. A watan Satumba na bana, majalisar dokokin kasar Amurka ta amince da nada Janar William Ward, tsohon mataimakin kwamandan sojojin Amurka a Turai a matsayin kwamandan hedkwatar bada umurni ta Afrika. Wannan hedkwatar bada umurni na kushe da mutane 120; A shekara mai zuwa kuma, za a kara su zuwa 800. An labarta cewa, a wannnan shekara, wata babbar tawagar wakilan ma'aikatar tsaron kasar Amurka ta kai ziyara a kasashe fiye da goma na Afrika da nufin shawo kan wadannan kasashe don su amince da shirin sojojin kasar Amurka na kafa hedkwatar bada umurni a Afrika da kuma neman wurin aiki na hedkwatar. Amma galilin kasashen sun yi watsi da shirin.
Wasu manazarta sun yi nuni da cewa, dalili na farko da ya sa kasashen Afrika suka ki yin haka shi ne, sun yi fargaban za a tauye cikakken mulkin kansu domin a ganinsu kafa hedkwatar bada umurni a Nahiyar Afrika zai samar da dama ga kasar Amurka wajen yin shisshigi cikin harkokin gida na kasashen Afrika. Kwanan baya bada jimawa ba, ministan harkokin waje na kasar Nigeria Mr. Ojo Maduekwe fafau ya bayyana damuwarsa. Cewa ya yi, kasashen Nahiyar Afrika ba su yin maraba da rundunar sojan kowace kasar waje; kuma girke sojojin kasar Amurka a Nahiyar Afrika zai keta mulkin kai na kasashen Afrika.
Dalili na biyu shi ne, a matsayin wata babbar kasa daya tilo mai kasaita fiye da kima a duniya, kasar Amurka har kullum takan daukar matakin soji don daidaita wassu matsaloli. Hakan ya karkata hankalin kasashen Afrika. Alala misali: a shekarar 2003, gwmanatin Bush ya tayar da yaki a Iraki har ya hamburar da mulkin Sadam ba tare da samun izni daga Majalisar Dinkin Duniya ba.
Dalili na uku wato na karshe shi ne, ko da yake wasu jami'an kasar Amurka sukan tofa albarkacin bakinsu kan kyakkyawar dangantakar hadin gwiwa tsakanin kasar Amurka da kasashen Afrika yayin da suke tabo magana kan hedkwatar bada umurni ta Afrika, amma kasashe da dama na Afrika sun yi imanin cewa, ainihin nufin kasar Amurka shi ne domin samun moriyarta kawai. Bisa shirin da aka tsara an ce, kasar Amurka za ta kafa sansanonin soja guda biyar a nahiyar Afrika. Gwamnatin Amurka ta sha yin ikirarin cewa wai ta kafa hedkwatar bada umurni ne ba domin yin tasiri da kuma yin ja-in-ja tsakaninta da sauran kasashe a Nahiyar Afrika ba. Amma kasashen Afrrika sun bayyana damuwarsu a kan cewa kasar Amurka za ta iya samun saukin sarrafa Nahiyar Afrika ta hanyar kafa hedkwatar bada umurni, musamman ma za ta iya kwace ikon mallakar albarkatun mai da kuma sauran makamantansu.
Jama'a masu sauraronmu, sanin kowa ne harkokin ta'addanci a duniyar yau, akan gudanar da su ne domin kasar Amurka da kuma sauran kasashen Yamma. Saboda haka ne, kasashen Afrika suke fargaban shiga irin wannan masifa muddin kasar Amuka ta kafa hedkwatar bada umurni ta sojojin kasar a nahiyar Afrika.
Ko da yake bangaren sojin Amurka ya sha alwashin ci gaba da yin shawarwari tare da kasashen Afrika da kuma zaben wurin aiki na hedkwatar a Afrika a karshe, amma ga alamu, da kyar kasar Amurka za ta cimma burinta idan ba ta kwantar da hankalin kasashen Afrika ba. ( Sani Wang )
|