Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-04 14:50:14    
Yankin musamman na Hongkong birni ne mai yawan dakunan ajiye kayayyakin tarihi

cri

Kodayake fadinsa ba shi da girma,wato ya kai muraba`in kilomita dubu daya da dari daya kawai,amma cibiyoyin jama`a masu ajiye kayayyakin tarihi dake karkashin shugabancin gwamnatin yankin musamman sun kai 13,ban da wannan kuma,akwai sauran dakunan ajiye kayayyakin tarihi da yawa kamarsu ma`adanar kayayyakin tarihi ta ilmin likitanci ta Hongkong da ma`adanar kayayyakin tarihi ta `yan sanda da ma`adanar kayayyakin tarihi ta al`adun jama`a na dan adam da sauransu,gaba daya sun kai fiye da 20 ko 30.

Tarihin kafa ma`adanar kayayyakin tarihi na Hongkong ya yi gajere sosai.A shekara ta 1962,an kafa ma`adanar kayayyakin tarihi ta farko ta Hongkong wato cibiyar ajiye kayayyakin fasahar zane-zane ta Hongkong.A shekara ta 1972,an raba wannan cibiya da kashi biyu wato suna hade da cibiyar ajiye kayayyakin fasahar zane-zane ta Hongkong da cibiyar ajiye kayayyaki ta Hongkong.Kawo yanzu,an riga an canja sunan cibiyar ajiye kayayyaki ta Hongkong wato sabon sunanta shi ne cibiyar ajiye kayayyakin tarihi ta Hongkong.

Cibiyar ajiye kayayyakin tarihi mafi girma ta Hongkong cibiyar ajiye kayayyakin tsaron lafiyar bakin teku ta Hongkong ce,fadinta ya kai muraba`in mita dubu 34,kayayyakin tarihin da wannan cibiya take ajiyewa suna da dogon tarihi har ya kai shekaru dari shida,wato tun daga daular Ming da daular Qing ta tsohuwar kasar Sin har zuwa yanzu.

Wadda ta fi kamara ita ce dakin ajiye kayayyakin tarihi na kabarin da ake kiransa da suna Lizhenwu,fadinta ya kai muraba`in mita dari daya da tamanin da biyar kawai,an tarar da kabarin Lizhenmu ne a shekara ta 1955,an kafa shi ne a zamanin Donghan na kasar Sin wato kafin shekaru kusan dubu biyu da suka shige,wannan ya nuna mana cewa,kakanin-kakanin mazaunan Hongkong sun riga sun yi zaman rayuwa a yankin nan cikin shekaru dubu biyu da suka shige.

Cibiyoyin ajiye kayayyakin tarihi na Hongkong suna da iri daban daban,alal misali,cibiyar ajiye kayayyakin tarihi na al`adun Hongkong wadda take ajiye da kuma yin bayani kan kayayyakin tarihi na al`adun wasan Yue,daya daga cikin wasannin gargajiya na kasar Sin ;da cibiyar ajiye kayayyakin tarihi na hanyar jirgin kasa ta Hongkong wadda ke ajiye tsofafin jiragen kasa iri daban daban ;da cibiyar ajiye kayayyakin tarihi na ilmin likitanci ta Hongkong wadda ke nuna mana cikakken tarihin bunkasuwar ilmin likitanci na Hongkong da dai sauransu.

Ban da wannan kuma,yankin Hongkong wata shaharariyar tashar teku ce a duniya,sha`anin jirgin ruwa yana da dogon tarihi,shi ya sa cibiyar ajiye kayayyakin tarihi na harkar teku ta Hongkong za ta bude kofa ba da dadewa ba.

Mun sami labari cewa,kwamitin tsare-tsare na Hongkong ya tsai da cewa zai ware kudin Hongkong miliyan 95 don kafa cibiyar ajiye kayayyakin tarihi na Sun Zhongshan,kuma cibiyar nan za ta bude kofa a farkon shekara ta 2007.Mr.Sun Zhongshan shahararen `dan juyin-juya-hali ne a tarihin kasar Sin.

Jama`ar Hongkong sun fi so su yi wa yaransu tarbiyya a wadannan cibiyoyi,a ko da yaushe ana iya ganin dalibai da yawan gaske su yi kallo a ciki.Wasu cibiyoyin ajiye kayayyakin tarihi na Hongkong su kan karbar `yan kallo ba tare da karban kudi ba.