Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-03 15:25:11    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (26/09-02/10)

cri

Yayin da taron wasannin Olimpic na Beijing na shekarar 2008 ke kara kusantowa,gidajen jakadu da kananan ofisoshin jakadu na kasar Sin dake wakilci a kasashen waje sun kara ba da muhimmanci kan aikin yin farfaganda kan wannan gaggarumin taron wasanni ga kasashen waje.A jajibirin ranar bikin kasa ta kasar Sin wato ran 1 ga watan Oktoba,bi da bi ne aka aika da kayayyakin yin farfaganda kan taron wasannin Olimpic iri daban daban kamarsu tambarin wasannin Olimpic na Beijing da kayan wasa na yaran nuna fatan alheri da takardar yin farfaganda kan wasannin Olimpic da ake kiranta da suna `sabon Beijing,sabon wasannin Olimpic` da hoto da CD da tuta masu yin farfaganda kan wasannin Olimpic da sauransu zuwa gidajen jakadu da kananan ofisoshin jakadu dake wakilci a kasashen waje.Hukumomin kasar Sin dake wakilci a kasashen waje suna yin farfaganda kan taron wasannin Olimpic yayin da ake taya murnar ranar bikin kasar Sin.Wannan shi ne karo na biyu da birnin Beijing da kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na birnin suka aika kayayyakin yin farfaganda zuwa kasashen waje bisa babban mataki a shekarar da muke ciki.

Don taya murnar shirya taron wasannin Olimpic,za a fara aikin tuka mota mai dogon zango tsakanin nahiyoyi uku daga watan Janairu na shekara mai zuwa,wato za a tuka mota daga Afirka zuwa Turai,daga baya kuma daga Turai zuwa nan Asiya,tsawon zangon nan zai kai kilomita dubu 40,a kan hanya kuma,za a gayyaci sinawa `yan kaka-gida fiye da dubu 10 saboda su sa hannu kan wata takardar musamman.A ran 16 ga watan Janairu na shekarar 2008,za a tuka motar kasar Sin daga `cape of good hope` dake kasar Afirka ta kudu,daga baya za a ketare kasashe fiye da 20 na nahiyar Afirka da ta Turai da ta Asiya wadanda suka hada da kasar Rasha,a watan Mayu na shekarar 2008,za a komo nan birnin Beijing.A kan hanya,za a yi farfaganda kan al`adun kasar Sin da taron wasannin Olimpic na Beijing da manufar dinkuwar kasa daya ta hanyar zaman lafiya ta kasar Sin,ban da wannan kuma,za a ba da kudin taimako ga wadanda ke bukata.

Kwanakin baya ba da dadewa ba,an shirya wani bikin nuna zane-zanen yaran kasashen duniya a birnin London na kasar Ingila,babban batun bikin nan shi ne kirarin taron wasannin Olimpic na Beijing wato `duniya daya,mafarki daya`.Yara sun zane taron wasannin Olimpic na Beijing dake cikin zuciyarsu a kan hotuna.Yara wadanda shekarunsu da haihuwa suka kai 10 zuwa 14 da suka zo daga kasashe da shiyoyyi 40 sun halarci bikin.(Jamila Zhou)