Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-03 15:22:29    
Babbar malamar koyarwa ta kungiyar wasan salon iyo ta kasar Sin kuma `Uwar wasan salon iyo` ta kasar Japan Masayo Imura

cri

Kawo yanzu,aikin share fage na taron wasannin Olimpic na Beijing ya riga ya shiga mataki na karshe,ayyukan gina cibiyoyi da filayen wasannin motsa jiki sun yi kusan kammala,yanzu dai ana yin bincike kansu,kungiyoyin wasanni daban daban na kasar Sin su ma suna sanya kokari matuka domin cim ma burinsu a gun taron wasannin Olimpic na shekara mai kamawa.A cikinsu,akwai wasu mutane wadanda suka zo kasar Sin daga kasashen waje domin ba da gudumawa ga sha`anin wasannin motsa jiki na kasar Sin wato sun kawo wa kungiyoyin kasar Sin tunanin zamani suna yin iyakacin kokari domin shiga taron wasannin Olimpic na Beijing tare da `yan wasan kasar Sin.Wadannan mutane su ne malaman koyarwa na kungiyoyin kasar Sin `yan asalin kasashen waje.Babbar malamar koyarwa ta kungiyar wasan salon iyo ta kasar Sin ta yanzu wato shahararriyar malamar koyarwa ta kasar Japan Masayo Imura ita ce daya daga cikinsu.A cikin shirinmu na yau,bari mu yi muku bayani a kanta.

Yayin da Masayo Imura take karatu a makarantar midil,sai ta fara koyon wasan salon iyo,bayan ta yi ritaya daga kungiyar wasan salon iyo a lokacin da ta kai shekarun 24 da haihuwa,ta fara aikinta na koyar da wasan.Daga nan ta yi kokarin yin nazari kan wasan,daga baya kuma ta kafa wata dabarar musamman ta atisaye.A karkashin horarta,matsayin `yan wasan salon iyo na kasar Japan ya dada daguwa bisa babban mataki.Kuma a karkashin kokarinta,`yan wasan salon iyo na kasar Japan sun samu lambobin zinariya 8 a gun taron wasannin Olimpic.Domin wannan,ana kiranta da sunan `uwar wasan salon iyo` ta kasar Japan.

A karshen shekarar 2006,Masayo Imura ta fara zama babbar malamar koyarwa a kungiyar wasan salon iyo ta kasar Sin bisa gayyatar da aka yi mata.Game da wannan,Masayo Imura ta ce:  `Dalilin da ya sa na karbi gayyatar kasar Sin shi ne domin `yan wasan kasar Sin sun gaya mini cewa,suna son samun lambobin yabo a gun taron wasannin Olimpic na Beijing,domin wannan,za su yi kokari matuka,kuma sun gaya mini cewa,suna bukatar sakamakona da jagorancina.`

Masayo Imura ta ce,kungiyar wasan salon iyo ta kasar Sin ta zabe ta da ta zama babbar malamar koyarwarta,wannan ya nuna mana cewa,`yan wasan kasar Sin suna amincewa da iyawarta,tana so ta yi kokari tare da su.

A karo na 12 na gasar cin kofin duniya ta wasan iyo da aka yi a birnin Melburne na kasar Australia a watan Maris na bana,wato watanni uku ke nan da Masayo Imuta ta fara aikin koyarwa a kungiyar kasar Sin,kungiyar wasan salon iyo ta kasar Sin ta samu sakamako mai faranta ran mutane,wato ta samu zama ta hudu sau hudu,amma a da,kungiyar kasar Sin ta samu zama ta shida sau biyu ne kawai.

Kan wannan,Masayo Imura ta dauka cewa,a gun gasar nan,kungiyar kasar Sin ta nuna wa kasashen duniya karfinta,kuma ta canja halinta a idon alkalan wasa.ana iya cewa,kungiyar wasan salon iyo ta kasar Sin wadda ke karkashin jagorancin Masayo Imura ta riga ta shiga wani sabon mataki.

A kwana a tashi,zumuncin dake tsakanin Masayo Imura da `yan wasan kasar Sin yana kara zurfafuwa,Masayo Imura ita ma tana kara kaunar `yan wasan kasar Sin.Ta ce: ``Yan wasan kasar Sin sun yi kokari,a wasu fannoni kuwa sun fi na `yan wasan kasar Japan.`

Daga ran 10 ga watan Mayu na bana,Masayo Imura ta fara yin kokari na mataki na karshe tare da `yan wasan kasar Sin domin shiga taron wasannin Olimpic na Beijing na shekara mai zuwa.Masayo Imura tana fatan `yan wasan salon iyo na kasar Sin za su samu zama ta farko a gasar duniya.Ta ce: `Taron wasannin Olimpic na Beijing yana zuwa,ina kokarin horar da `yan wasan kasar Sin,nufina shi ne zakarar Asiya ko kugniyar kasar Sin ko kungiyar kasar Japan za ta samu zama ta farko a duniya.Muna yin kokari domin cim ma burin nan.`

Kodayake yanzu matsayin `yan wasan salon iyo na kasar Sin bai kai na `yan wasan kasar Rasha da kasar Japan ba,amma sharadin jikinsu yana da kyau sosai,shi ya sa ana fatan `yan wasan kasar Sin za su samu lambar zinariya a gun taron wasannin Olimpic na Beijing. (Jamila zhou)