An fara gudanar da "dokar ikon mallakar dukiyoyi" daga ran 1 ga watan Oktoba wato ranar bikin kasa ta kasar Sin. "Dokar ikon mallakar dukiyoyi" doka ce ta farko da kasar Sin ta tsayar kan dukiyoyin jama'a masu zaman kansu. Dokar nan za ta shafi moriyar fararen hula biliyan 1.3 wadda kuma aka shafe shekaru 14 ana shirin kaddamar da ita ta fito ne daga kyayyawan halin zaman al'umman kasar da zaman jin dadin jama'a, kuma ta tabbatar da manyan sauye-sauyen da aka samu a kasar Sin wajen kiyaye ikon mallakar dukiyoyi.
Bisa matsayinta na mai bayyana dangantakar da ke tsakanin mutane da dukiyoyinsu, "dokar ikon mallakar dukiyoyi" ta tsai da muhimman ka'idoji wajen mallakar dukiyoyi da yin amfani da su da samun moriya daga wajen su, sabo da haka dokar ta zama wani muhimmin kashi wajen tsai da babbar dokar jama'a. A lokacin da Mr. Wu Bang'guo, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya tabo magana kan babbar ma'ana ta dokar, ya bayyana cewa, "Aikin tsai da "dokar ikon mallakar dukiyoyi" yana da muhimmiyar ma'ana ga kyautata tsarin mallakar dukiyoyi na kasar Sin mai sigar musamman ta gurguzu, da tsayawa ga bin tsarin tattalin arziki na gurguzu, da bunkasa tattalin arzikin kasuwanni na gurguzu, da kiyaye babbar moriyar jama'a, haka ma ga kara karfin kagowa na duk zaman al'umma."
Bayan da kasar Sin ta shafe shekaru kusan 30 tana yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, tattalin arzikin kasar ya samu bunkasuwa da sauri wanda kuma ya jawo hankalin duk duniya baki daya, ba idin haka kuma yawan dukiyoyin da fararen hula na kasar Sin suke mallaka ya karu-karuwar gaske. Sun Xianzhong, shahararen masanin ilmin dokoki na kasar Sin, kuma shehun malamin ofishin binciken ilmin dokoki na cibiyar binciken kimiyya ta zaman al'ummar kasar ya bayyana cewa, "Kasarmu ta shafe shekaru fiye da goma tana yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, dukkan mutane suna cewa manufar da jam'iyyarmu ta tsayar tana da kyau, a hakika kuwa wannan manufa tana nufin cewa ya kamata a amince da ma'aikata suna da ikon mallakar sakamakon aikinsu".
A lokacin da Mr. Wang Zhaoguo, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na J.K.S. kuma mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya tabo magana kan sauyawar tunanin mutane wajen kiyaya ikon mallakar dukiyoyi ya bayyana cewa, "Bisa ci gaban tattalin arziki da kyautatuwar zaman jin dadin jama'a, yawan dukiyoyin da jama'a masu zaman kansu suke mallaka sai kara karuwa yake, musamman ma jama'a sai kara yawa suke suna ta mallakar kayayyakin kawo albarka na kansu, sabo da haka jama'a suna kara bukatar kiyaye dukiyoyinsu ta hanyar yin amfani da dokoki."
Mr. Wang Yang, CEO wato babban jami'in zartaswa na tsarin internet din sa ido kan ayyukan yin tsimin makamashi na kasar Sin ya bayyana cewa, "Wasu dokokin kasar Sin taka rawa wajen kiyaye dukiyoyi na masana'antu masu zaman kansu, wannan ya zama wani abu mai kyau gare mu ".(Umaru)
|