Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-02 14:48:13    
Irin damisa da ke zama a manyan duwatsu na Xingan da Changbai a arewa maso gabashin kasar Sin

cri

Damisa yana daya daga cikin dabobbi da ke dab da karewa da sauri a doron duniya. Irin damisa da ke zama a manyan duwatsu na Xingan da Changbai a arewa maso gabashin kasar Sin suna da girman jiki da kwarjini da kuma kyakkyawan gashi mai walkiya, idan an kwatanta shi da sauran ire-iren damisoshi na duniya, sai a ce, shi sarkin damisa ne.

An gina gandun kiwon irin wannan damisa na kasar Sin ne a karkarar arewacin birnin Harbin na lardin Heilongjiang da ke a arewa maso gabashin kasar Sin. Yawan damisoshi da ake kiwo a wannan gandu ya zarce arbamiyya, gandun nan kuwa gandun kiwon damisoshi ne mafi girma a duniya. A safiyar wata rana ta farkon yanayin bazara, wakilanmu sun tashi daga birnin Harbin, bayan da suka yi doguwar tafiya, sun isa wannan gandun kiwon damisoshi. Fadin gandun nan ya kai kimanin kadada uku. A nan ne suka ga damisoshi da yawa da ke yawo a cikin dazuzzuwa ko bakin kwari da ruwa ya daskare, wasunsu kuma suna karya kumallo cikin hasken rana.

An kasa damisoshi cikin wurare 8 da aka yi musu shingen karfe bisa shekarunsu da haihuwa. Malam Du Minxian wanda shi ne jagoran gandun nan ya shafe sama da shekaru 10 yana aiki a gandun. Babban aikin da yake yi a ko wace rana shi ne zagayawa a gandu cikin motar Jeep. Ya kan jefa abinci domin damisoshi, kuma yana kula da kananan damisosahi. Ya san duk damisoshi da ke cikin gandunsa, ya iya bambanta lambobin duk damisoshi da kuma lakabansu. Ya bayyana wa wakilanmu cewa, "da farko, a dubi kamannin fuskarsu, kana a ga siffar girarsu, sa'an nan kuma a bambanta launuka da siffofin gashinsu. Ban da wadannan kuma yayin da suke kai da kawowa, daidai kamar mutane, motsin jikinsu ba iri daya ba ne, haka karkada wutsiyarsu."

Kare maganar Du Minxian ke da wuya, sai motarmu ta isa cibiyar wurare da damisoshi su kan kai da kawowa. Nan take akwai kimanin damisoshi 20 wadanda nan da nan suka taru a kewayen motarmu da aka yi mata kariya na karfe a jikinta. Wasunsu sun tsallake kan rufin motar, suna neman nama da za a ba su. Malam Du ya bayyana wa wakilanmu cewa, babban aikin motar da muke ciki shi ne bai wa damisoshi abincinsu, damisoshi kuma suna da hazikanci, da sun ji karar motarmu daga wuri mai nisa, to, sun san za a ba su nama ne su ci. A halin yanzu, a kan bai wa damisoshi nama ko kaji masu rai su ci a wannan gandun kiwon damisoshi, a wani sa'i ma a ba su shanu ko rago su ci. Akwai masu yawon shakatawa da yawa wadanda suke zuwa gandun nan musamman domin kallon yadda tamisoshi ke kama shanu ko rago ko kaji su ci.

Yanzu, yawan masu yawon shakatawa da ake iya karba a wannan gandu ya kai darurruka a ko wace rana. A cikin gandun nan, wakilanmu sun tarar da wata 'yar yawon shakatawa mai suna Jiang Shu wadda ta fito daga birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin. Ta gaya wa wakilanmu cewa, "irin wannan damisa da ke zama a arewa maso gabashin kasar Sin suna dab da karewa a doron duniya. Sabo da haka suna da daraja kwarai. Gandun nan mai girma ne sosai. Dazu, mun ga irin hanyar da ake bi wajen kiwonsu bakon abu ne gare ni, kuma ya yi kwaikwayon yadda damisoshi ke zama a dazuzzuka. Mu masu yawon shakatawa muna sha'awarta ainun. Mai yiwuwa ne, a karo na farko masu yawon shakatawa suka sami damar kallon wannan. "

Bisa kimantarwa da 'yan kimiyya suka yi, an ce, yawan damisoshi irin na kasar Sin wadanda ke zama a dazuzzuwa bai wuce 500 a duniyar yanzu ba. Babban manajan wannan gandu Malam Wang Ligang ya bayyana wa wakilanmu cewa, makasudin kafa gandunmu shi ne domin gudanar da harkokin yawon shakatawa, kuma musamman domin mayar wa damisoshi rayuwar daji.