Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-01 16:00:14    
Wasu labaru game da kabilun kasar Sin

cri

Jihar Tibet wata kasa ce mai al'ajabi, mutane suna sha'awar duwatsu da tabkuna da addini da dakunan ibada na Tibet kwarai da gaske. Yawancin mutanen Tibet suna bin addinin Buddha, hanyarsu ta nuna biyaya ga addini ita ce shiga cikin dakin ibada don zama 'yan addinin Buddha da ke zama a ciki. A cikin shirinmu na yau za mu kai ku zuwa cikin dakunan ibada na addinin Buddha.

Losancairan wani dan addinin Buddha ne da ya bar gida ba da jimawa ba, yana da shekaru 14 da haifuwa. A lokacin wakilin gidan rediyon kasar Sin ya gan shi a gaban dakin ibada na Zheban a karkarar birnin Lasa, yana shanya rana tare a abokansa, kuma yana kallon masu ziyara, sai wakilin ya yi hira da shi kan zamansa a cikin dakin ibada.

Ya gaya wa wakilin cewa, zamansa a cikin dakin ibada ya yi kama da zaman da a ke yi a makaranta, wato ana ba su darassi a kowace rana, musamman ana ba su darassin harshen Tibet da littattafan addinin Buddha. Ban da haka kuma suna da harkoki daban daban misali buga kwallon kafa da kwallon kwando, kuma suna iya karanta sauran litattafai. Ya ce,

Muna da rediyo, muna iya saurara shirye shiryen gidan rediyo na harshen Tibet da harshen Han, na fi son kallon sinima na wasan dambe da wasannin kwaikwayo, na riga na yi zama a nan cikin shekaru 3, zan ci gaba da yin karatu a nan har fiye da shekaru 10.

Bayan da muka yi hira da Losan mun ga wadannan kananan addinin Buddha sun dauki dakin ibada a kama da makaranta. Hasali ma haka ne, ba tun yau ba 'yan kabilar Tibet sun dauki dakunan ibada a kama da wuraren samun ilmi. Idan 'yan kabilar Tibet suna son samun ilmi dole ne su shiga cikin dakunan ibada.

Ban da irin litattafan addinin Buddha kuma 'yan addinin Buddha da ke zama a dakunan ibada za su iya karanta littattafan da su ke so, kuma suna iya zabi mallaman koyarwa. Mallaman koyarwa na dakunan ibada duk sheffan mallamai ne, aikinsu ba ba da ilmi kawai ba, kuma suna koya musu yadda za su zama mutanen kirki.

Mr. Duorang wani mallami ne na dakin ibada na Zhebang, aikinsa shi ne koyar wa kananan 'yan addinin Buddha littattafan addini, ya yi hira da wakilinmu kan aikinsa cewa,

Mu kan tashi a karfe 5 da rabi da safe a ko wace rana, sa'an nan mu je babban daki don karanta littattafan addini, sa'an nan na fara ba da darassi, da yamma ma zan ba da darassi, da dare ya yi sai 'yan addinin Buddha su yi karatu su da kansu. Dalibai suna da kwazo da himma a wajen karatu, shi ya sa na ji dadi da aikina.

Ban da karatu 'yan addinin Buddha da ke zama a cikin dakunan ibada kuma su kan yi harkokin addinin Buddha. Addinin Buddha yana da bukukuwa da yawa, sabo da haka su kan yi sharye shirye sabo da irin wadannan bukukuwa. 'yan addinin Buddha su kan koyi raye raye na addinin da hada littattafai da yi kayayyakin da a ke amfani da su a gun bukukuwa.

Yanzu zamani ya sake, 'yan addinin Buddha da ke zama a cikin dakunan ibada suna da zabi da yawa, wato ban da karatu kuma suna iya yin abubuwan da su ke sha'awa. Misali yanzu dakunan ibada sun zama wuraren da masu ziyarar yawon shakatawa ke sha'awa, sabo da haka 'yan addini sun zama jagorar masu ziyarar yawon shakatawa.