Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-01 15:51:19    
Sun yi amfani da shi wajen jigilar kaya da daukar mutane, ta yadda suka samu kudi masu yawa

cri

He Yanmei, manomiya ce mai shekaru 35 da haihuwa da ke lardin Henan. Ko wace rana da asuba, mijinta ya kan hau kekensa mai taya 3, ya je jigilar kayayyaki. An sayi keken ne a shekarar 2003 da rancen kudi yuan dubu 2 wanda suka samu daga kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta ba da taimako ga matalauta. He Yanmei ta ce, bashin da suka ci yana da amfani, tun da suka sayi keken, sun yi amfani da shi wajen jigilar kaya da daukar mutane, ta yadda suka samu kudi masu yawa.

'Saboda keken, ko wace rana a kalla dai na kan samu yuan hamsin, wani lokaci ma yana sama ya kai yuan dari 2, wannan ba kudin kadan ne ba cikin kauyuka. Gaskiya ne rancen kudin nan da aka bayar yana da amfani.'

Game da mutane da ke zaune a cikin manyan birannen kasar Sin, yuan dubu daya biyu kudi kalilan ne. Amma dangane da mutanen da ke kauyuka masu fama da talauci, kudin zai iya ba da taimako wajen fitar da su daga halin da suke ciki. A da, gundumar Nanzhao da He Yanmei ke zaune tana da komabaya wajen tattalin arziki. Amma, cikin shekarun nan, mutanen wurin sun yi amfani da rancen kudi da gwamnati ta bayar wajen jigilar kayayyaki da kiwon kifaye da dabbobi da kuma dasa itatuwa, sun samu sauye-sauye wajen zaman rayuwarsu.

Wanda yake bayar da rancen kudi a madadin gwamnati shi ne kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta ba da taimako ga matalauta da ke gundumar Zhaonan. Gao Changyuan, shugaban kungiyar ya gaya wa maneman labaru cewa,

'An fara bayar da rancen kudi a garinmu tun daga shekarar 1995. Gwamnatin kasarmu ta samo bashin nan ne daga assusun da ke kasashen ketare. Bayan shekaru 10, a garinmu an riga an bayar da rancen kudi fiye da yuan miliyan 65, yawan iyalan manoma da suka ci bashin ya kai 7715.'

Sabo da za a iya mayar da rancen kudin sannu a hankali, manoma suna kaunarsa kwarai. He Yanmei ta ce, mutanen garinta dukansu sun nuna yabo ga bashin da aka bayar.

'Mun iya biyan bashin da muka ci sannu a hankali cikin lokaci dabam daban, wannan ya taimaka. Ka sani, a cikin kauyuka da kyar za a iya samun kudi masu yawa cikin lokaci kadan. Shi ya sa ina farin ciki sosai da aka yarda mu mayar da kudi cikin lokaci mai tsawo.'

Yanzu a fadin kasar Sin, ya kasance da kungiyoyi faye da dari wadanda ke bayar da rancen kudi ga manoma, kamar yadda kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta ba da taimako ga matalauta ta gundumar Zhaonan take yi. Rancen kudin da suka bayar sun kai yuan biliyan, kuma yawancinsu sun zo daga kasashen ketare, wasu su ne kudin taimako da aka bayar, wasu kuma rancen kudi ne tare da ruwa kalilan.

Sabo da manoman kasar Sin sun samu moriya daga wajen rancen kudin, kuma su kan mayar da kudi cikin lokaci, kungiyoyi dabam daban kamarsu bankin duniya da hukumar shirin raya kasa ta MDD wadanda ke ba da kudi, sun nuna yabo ga kasar Sin. Wasu daga cikinsu kuma sun kara ba da kudi ga kasar Sin. Ga misali, kamfanin Citigroup ya taba bayar da dalar Amurka miliyan 1.3 ga kasar Sin kamar kudin taimako, kwanakin baya ya kara ba da dalar Amurka yuan miliyan 1.5 ga kasar Sin kamar kyauta.

Kwararru kan al'amuran kauyuka na kasar Sin suna fata kungiyoyin kasa da kasa za su ci gaba da bayar da kudin taimako ga kasar Sin domin kyautata zaman rayuwar manoman kasar Sin.