Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-28 18:21:47    
Labari kan wasannin motsa jiki da wani dan jarida yake da masaniya a kai

cri

Aminai 'yan Afrika, a cikin da'irar 'yan jarida na wasannin motsa jiki na kasar Sin, ba wanda bai san Mr. Gao Dianmin ba, wanda ya zama dan jarida na farko na kasar Sin da ya bayar da wani muhimmin labari a kan cewa " Kasar Sin ta samu lambar zinariya ta farko a tarihin tarurrukan wasannin Olympics" a gun taron wasannin Olympic na 23 na Los Angeles a shekarar 1984. Yanzu, Mr. Gao Dianmin ya rigaya ya kama mukamin daraktan sashen edita na wasannin motsa jiki na Kamfanin Dillancin labaru na Xinhua, bugu da kari ya zama mamban kwamitin watsa labarai na kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa. Kawo yanzu dai, Mr. Gao Dianmin ya riga ya dauki labarai a gun tarurruka shida na wasannin Olympics da aka gudanar a da wato daga taron wasanin Olympics na 23 na shekarar 1984 zuwa taron wasannin Olympics na Aden na shekarar 2004. Yayin da ya kai shekaru 30 da haihuwa ya soma daukar labarai a karo na farko a shekarar 1984. A wancan lokaci, an ba Mr. Gao Dianmin mai kuruciya aikin daukar labarai game da wasan harbe-harbe. Daidai a wannan fannin wasa ne dan wasa mai suna Xu Haifeng na kasar Sin ya lashe abokan karawarsa har ya sami lambar zinariya ta farko ta kasar Sin a gun taron wasannin Olympics. Mr. Gao ya ruwaito wannan labari daidai kuma cikin lokaci a kan cewa " Lambar zinariya ta farko ta kasar Sin a taron wasannin Olympics". Saboda haka, ya yi suna a cikin gidan kasar da kuma wajenta a matsayin wani shahararren dan jarida na wasannin motsa jiki. Idan ya yi waiwayen lamarin na wancan lokaci, sai ya jiku sosai, yana mai cewa: " A matsayin wani dan jarida na Kamfanin Dillanci Labaru na Xinhua, na yi alfaharin samun damar daukar labarai a karo na farko a gun taron wasannin Olympics da aka gudanar a shekarar 1984, inda na gane ma idona yadda dan wasa Xu Haifeng ya karya matsayin rashin samun lambar zinariya ko daya na kasar Sin a tarihin tarurrukan wasannin Olympics".

Jama'a masu sauraro, ko kuna sane da cewa, tun bayan da kasar Sin ta sake koma wa babban iyalin wasannin Olympic a shekarar 1979, sai ta nuna himma da kwazo wajen shiga taron wasannin Olympics. Taron waannin Olympics na Los Angeles na shekarar 1984, taron wasanni ne na yanayin zafi na Olympics, wanda kuma a karo na farko ne kasar Sin ta aike da 'yan wasa don halartar taron wasannin bayan da aka maido da kujerar kasar Sin a cikin kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa. Da yake aka gudanar da wannan gagarumin taron wsannin Olympics na Los Angeles a yankin kasar Amurka, don haka aka samu kyakkyawan dandalin musanye-musanye da kuma kara dankon zumunci tsakanin kasashen Sin da Amurka.

Jama'a masu sauraro, kun san cewa, a gun wasu tarurrukan wasannin Olympics da aka gudanar bayan taron wasannin Olympic na Los Angeles, kungiyar wakilan kasar Sin ta kara kasaita har ta samu maki mai armashi. Sakamakon haka ne dai, Sinawa suka bullo da nufin rokon gudanar da wani gagarumin taron wasannin Olympics a bakin kofar gidansu. Ko da yake ba a cimma burinsu a shekarar 1993 ba, amma ba su karaya ba, akasin haka, sun yi shiri sosai sun kuma gabatar da rokon samun iznin gudanar da taron wasannin Olympic na 29 na yanayin zafi na shekarar 2008 a hukumance. A ran 13 ga watan Yuli na shekarar 2001, gwamnatin birnin Beijing ta cimma burinta na samun wannan kyakkyawar dama. Mr. Gao Dianmin ya yi farin ciki da fadin cewa: " A lokacin da gwamnatin birnin Beijing ta gabatar da rokonta a karo na biyu na shirya taron wasannin Olympics, na je Moscow tare da wasu mahukuntan gwamnatin birnin bisa gayyatar da aka yi min don shiga aikin gabatar da rokon. Da Mr. Samaranch ya kammalar shelar Beijing da za ta shirya taron wasannin Olympic, sai na jiku kwarai da gaske, lalle babu wata kalmar dake iya siffanta halin zuciyata. Wasu 'yan jaridu na kasashen Yamma su ma sun kewaye ni domin taya murna".

Nasarar samun iznin shirya taron wasannin Olympic da birnin Beijing ya yi na nufin cewa, za a gudanar da taron wasannin Olympics a kasar Sin a karo na farko a cikin tarihin Olympic na zamanin yanzu. Babu tantama, wannan babban lamari ne na tarihin al'ummar kasar Sin.

A matsayin wani muhimmin kamfanin dillancin labaru na mai masaukin taron wasannnin na Beijing, kamfanin dillancin labaru na Xinhua na daukar babban nauyin dake bisa wuyansa na bayar da labarai ga masu sauraro da kuma masu kallo na gida da na waje. Game da wannan dai, Mr. Gao ya fadi cewa: " A ganina, yin aiki da kyau na bayar da labarai game da taron wasannin Olympics, ba wai kawai yana nufin cewa za a bayyana nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin siyasa, da tattalin arziki da kuma na al'adu da da sauran fannoni ba, har ma za a bayyana yadda kasar Sin take bunkasa sha'anin wasannin motsa jiki". ( Sani Wang )