Ran 2 ga wata, a birnin Osaka na kasar Japan, an rufe gasar fid da gwani ta wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasa da kasa a karo na 11, inda kungiyar kasar Sin ta zama ta 10 saboda samun lambar zinariya daya da ta azurfa daya da kuma ta tagulla daya.
Har kullum wasan guje-guje da tsalle-tsalle muhimmin wasa ne mai yawan lambobin zinariya a gun taron wasannin Olympic. Gasar fid da gwanni ta kasa da kasa da aka yi a Osaka, gasa ce ta karshe wajen jarrabawa da kuma horar da 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle daga dukkan fannoni kafin taron wasannin Olympic na Beijing a shekara mai zuwa. Shi ya sa dai galibin 'yan wasa na matsayin koli na duk duniya suna shiga wannan gasa. 'Yan wasa 57 na kasar Sin sun shiga kananan wasanni 25 don neman zama zakara, wadanda yawansu ya karya matsayin bajimta na kasar Sin wajen shiga wannan muhimmiyar gasa ta duniya.
A cikin dukkan wadannan 'yan wasan Sin, lambar zinariya da Liu Xiang ya samu a cikin gasar gudu tare da ketare shinge mai tsawon mita 110 ya fi ba mutane zumudi, saboda ita ce lambar zinariya ta farko da 'yan wasan Sin maza suka samu a tarihin gasar fid da gwani ta wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya, haka kuma lambar zinariya ce da kasar Sin ta sake samu bayan shekaru 8 a gun wannan gasar, sa'an nan kuma, ita ce kacal da 'yan wasan Asiya suka samu a wannan karo.
Bayan da ya zama zakara a gun taron wasannin Olympic da gasar fid da gwani ta duniya da kuma rike matsayin bajimta na duniya, makasudi na gaba da Liu Xiang ya tsara shi ne neman sake zama zakara a gun taron wasannin Olympic na Beijing. Liu Xiang ya ce,'A idon ko wane dan wasa, zai yi da na sani in bai shiga taron wasannin Olympic ba. A gare mu kuma, mun yi farin ciki saboda shiga taron wasannin Olympic a mahaifiyarmu kasar Sin. Bisa makin da muka samu, sannu a hankali ne za mu sami ci gaba, na yi imanin cewa, za mu shiga gasar karon karshe.'
Game da taron wasannin Olympic na shekara mai zuwa, ba tare da boye kome ba malam Sun Haiping, wanda ke horar da Liu Xiang, ya ce, suna fuskantar babbar matsin lamba, amma zai kara yin ayyuka daga dukkan fannoni ta hanyar kimiyya don tabbatar da ganin cewa, 'yan wasan Sin maza na ci gaba da zama kan gaba a cikin gasar gudun ketare shinge mai tsawon mita 110.
Babban malamin horas da wasanni na kungiyar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasar Sin malam Feng Shuyong ya yi bayani kan sakamakon da kungiyar kasar Sin ta samu a wannan karo, ya ce,'Sakamako mafi girma da muka samu a wannan karo shi ne imani. Za mu sami maki mai kyau in muna da imani, kuma muna gudanar da ayyuka yadda ya kamata. Sakamako na biyu shi ne bayan da 'yan wasanmu suka shiga irin wannan muhimmiyar gasar duniya kafin taron wasannin Olympic, musamman ma sun yi gasa a Osaka, wadda ta yi kama da Beijing a fannonin bambancin lokaci da yanayi da halin zaman rayuwa, mun gano dimbin abubuwan kasawa, wadanda suka yi farga da mu cikin lokaci. Hakan ya ba mu damar kara horar da 'yan wasanmu daidai bisa tsarin da aka tsara a cikin shekara daya da ta rage a gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing.'
A zahiri kuma, gasar fid da gwani ta duniya ta Osaka ta tono abubuwan kasawa masu yawa da kasar Sin ke fuskanta a wasan guje-guje da tsalle-tsalle. Game da wannan, malam Feng ya ce,'Ko da yake mun sami lambobin yabo 3, haka kuma makin da kungiyarmu ta samu ya fi wanda ta samu a gasar da ta gabata, amma duk da haka, kada mu yi farin ciki. Muhimmin aikinmu shi ne ko yaya makin da ya samu, wajibi ne ko wane dan wasa da malamin horas da wasanni ya gano abubuwan kasawa. Bisa halin da ake ciki a yanzu, wasu 'yan wasanmu sun rasa isassun nagartattun fasahohi a lokacin da suke neman samun maki mai kyau, suna kuma koshin lafiya a fannin tunani. Nan gaba za mu mai da hankali kan yadda za a horar da 'yan wasanmu bisa bukatun muhimman gasannin duniya a tsanake yadda ya kamata. Kada mu dogara da takin sa'a kawai wajen samun maki mai kyau, in ba haka ba, ba za mu sami isasshen tabbaci ba.'
Malam Feng ya kara da cewa, kungiyar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasar Sin na bukatar yin dimbin ayyuka don sami maki mai kyau a taron wasannin Olympic a shekara mai zuwa.(Tasallah)
|