Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-25 15:47:17    
Babban gidan wasan kwaikwayo na Shanghai da kuma wurin adana halittun teku na Shanghai

cri

Wannan gidan wasan kwaikwayo ya hada da dandamali guda 3, wato da farko, wani babban dandamali, inda mutane 1800 ke iya kallon rawar ballets da sauraren wasan kwaikwayon waka da kide-kide, na biyu kuma, wani matsakaicin gidan wasan kwaikwayo, inda masu sauraro ke iya jin dadin sauraren kide-kide, na uku kuma, wani karamin gidan wasan kwaikwayo, inda mautane ke iya kallon wasannin kwaikwayo da nune-nunen tufafi. Masu sauraro ko kuma 'yan kallo da ke zaune a ko wace kusurwar babban dandamali suna iya sauraren ko wace kalma da masu nuna wasan kwaikwayo suka fada.

Wurin adana halittun teku na Shanghai wani gini ne daban na zamani a Shanghai. A matsayin wurin adana halittun teku mafi girma a Asiya, wurin adana halittun teku na Shanghai da ke dab da hasumiyar telibijin na Dongfangmingzhu yana da dogon rami mai tsawon mita 155 mafi tsawo a kasar Sin, inda masu yawon shakatawa ke iya kallon hallitun teku a karkashin ruwa. An raba wannan wurin adana halittun teku zuwa sassa 8, inda ake nuna kifaye masu daraja ire-ire 28 fiye da 10,000 da suka zo daga nahiyoyi 4 da tekuna 5.(Tasallah)


1 2