Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-24 15:04:28    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- Kauyen Zhongzhai na kabilar Zhe wato manyan dakuna masu kyaun gani na iyalin Zhong da ke shiyyar Daoneihuli ta birnin Xiamen da ke lardin Fujian na kasar Sin yana ta kara jawo hankulan mutane sabo da al'adun kabilar She wanda yake hade da al'adun "Dacuozhongzhai" mai daraja na kabilar She da ke kudancin lardin Fujian.

Da akwai mutane 'yan kabilar She fiye da 3000 wadanda ke zaune cikin wannan "kauyen da ke cikin birnin", inda aka kiyaye tsoffin gidaje masu daraja na iyalin Zhong, wannan kuma ya bayyana kyakkyawan halin jituwar da ake ciki a wannan birni na zamani wato birnin Xiamen.

Unguwar kabilar She ta manyan dakunan iyaliyan Zhong da ke shiyyar Huli, da kauyen musulmin na Chentang da ke shiyyar Xiang'an sun zama unguwoyi 2 ne masu cunkushe da 'yan kananan kabilu da ake da su kawai a birnin Xiamen. Bisa kididdigar da hukumar kula da zaman lafiya ta wannan birnin Xiamen ta yi an ce, ya zuwa watan Afril na shekarar da ta wuce, yawan kananan kabilun da ake da su a birnin ya kai 44, yawan mutanensu kuma ya wuce 27000, daga cikin su kuma da akwai mutane fiye da 10000 wadanda suka zo daga sauran wurare, wadanda kuma ke zama a nan cikin dan lokaci.

Ban da wannan kuma birnin Xiamen tana kulawa da 'yan kananan kabilu sosai wajen aikin kawo albarka da zaman rayuwarsu, cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, ya ware kudin Sin fiye da Yuan miliyan 7 domin kafa makarantun firamare na kabilar She da na kabilar Hui wato musulmi.

---- Bayan shekaru fiye da 230 da aka yi kaura zuwa kwarin kogin Yili na jihar Xinkiang da ke yammacin kasar Sin, har ila yau jikokin 'yan kabilar Xibo, daya daga cikin kananan kabilun kasar Sin suna rike da fasahar gargajiya ta yin "kibiya mai kararrawa". Yanzu kuma an shiga da wannan fasaha cikin sunayen ayyukan da M.D.D. ke yi domin yaki da kangin talauci.

"Kibiya mai kararrawa" wata irin kibiya ce, a galibi dai akan yi amfani da ita domin tsaron kai ko yin farauta, bayan da aka harba irin wannan kibiya, sai sautin usur ya tashi.

Ayyukan yaki da kangin talauci da raya shiyyoyin da 'yan kananan kabilu ke zama wadanda ake gudanar da su bisa jarin da hukuma shirin raya kasa ta M.D.D. da kwamitin kula da harkokin kabilu na kasar Sin suka zuba tare, yawan kudin da suka zuba kuma ya kai dalar Amurka miliyan 7. An yi wannan aiki ne musamman ta hanyar kafa tsarin ba da taimako don sa kaimi ga bunkasa shiyyoyin da kananan kabilu ke zama. Cikin watan Agusta na wannan shekarar da muke ciki, kungiyar ba da taimako ga 'yan kananan kabilu domin yaki da kangin talauci da raya kasa ta M.D.D. ta tabbatar da cewa, fasahar yin "kibiya mai kararrawa" ta kabilar Xibo ta zama daya daga cikin ayyukan da za a bunkasa su domin yaki da kangin talauci.(Umaru)