Aminai 'yan Afrika, lallai ba ku manta ba a shekarar 2001 wato lokacin da birnin gwamnatin Beijing ta kasar Sin ta yi nasarar samun iznin shirya taron wasannin Olymmics na Beijing a shekarar 2008 ba; kuma dukkanku kun san cewa ran 8 ga watan Agusta na wannan shekara rana ce da cika shekara guda da ta rage a gudanar da wannan gagamin taron wasannin. To, yanzu sai ku gyara zama don ku saurari wani labari mai ban sha'awa a game da wata 'yar makarantar sakandare na birnin Beijing, sunanta Zhang Le. ' Sannu aminai ! Ni ce Zhang Le dake yin karatu a aji na uku na wata makarantar sakandare mai suna ' Ba Yi' ta nan birnin Beijing. Ma'anar sunana ita ce farin ciki'.
An haifi Zhang Le ne a watan Agusta na shekarar 1990 a wani iyalin masana na birnin Beijing. Lallai fitowarta a duniya ta kawo wa iyayenta farin ciki, wadanda kuma suka nada mata wannan suna ne domin fatan diyarsu za ta yi farin ciki har abada dundundun. A ran 22 ga watan Satumba na shekarar 1990, an gudanar da taron wasannin watsa jiki na 11 na Asiya cikin gagarumin hali a nan Beijing. A lokacin, shekarun Zhang Le ta kai wata guda kawai bayan haihuwarta. Iyayenta suna kula da ita kuma suna kallon gasanni masu ban sha'awa. Ba mai yiwuwa ne wadannan gasanni su bai wa Zhang Le wata alama a cikin zuciyarta. Amma mamanta ta fadi cewa, ' A lokacin, gasannin da aka watsa ta Telebijin sun kasance tamkar wani abu ne da Zhang Le ta taba bayan ta zo wannan duniya'.
Aminai 'yan Afrika, lallai ba ku manta ba, a gun cikakken zama na 112 na kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa da aka gudanar a ran 13 ga watan Yuli na shekarar 2001 a Moscow, gwamnatin birnin Beijing ta samu iznin gudanar da taron wasannin Olympics na Beijing a shekarar 2008. A lokacin da shugaba Samaranch na kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa ya fito da kalmar Beijing, nan take halin annashuwa ya game duk unguwar da Zhang Le ke zaune, inda mazauna unguwar suka yi sowwa cewa ' Beijing ta ci nasara' ! ' Mun samu nasara' ! Karamar Zhang Le ita ma ta yi farin ciki matuka, ta yi tafin hannu tana maimaita kalmar ' Beijing, Beijing.' Amma ta yi mamaki da ganin yadda mamanta ta yi. Zhang Le ta furta cewa : ' Na yi farin ciki da yin kirarin cewa ' Beijing, Beijing' a gaban akwatin telebijin. A lokacin, ina so in kirayi mamata da ta je tare da ni domin taya murnar lamarin. Amma na ga mamata ta zubar da hawaye. Hakan ya ba ni mamaki. Bayan na girma, sai na gane me ya sa mamata ta yi hakan. Duk wadanda ba su taba jure wa bacin rai da aka samu sakamakon rashin cimma burin samun damar shirya taron wasannin Olympics a shekarar 1993 ba, da kyar za su iya gane irin farin ciki da kuma alfarma da aka yi bayan da aka samu iznin shirya taron wasannin Olympics na Beijing a shekarar 2008. Yanzu, ina karatu a wata makarantar gwaje-gwajen wasannin Olympic, inda kuma aka gina wani dakin horar da 'yan wasa na Olympics a nan. Duk wadannan abubuwa sun fadakar da ni a game da hasashen wasannin Olympics. Zhang Le ta fadi cewa : ' Ko da yake mun samu matsala sakamakon ayyukan gine-gine da ake yi a nan makarantarmu, amma mun yi farin ciki matuka domin a wannan lokaci na shekara mai zuwa wasu shahararrun taurari 'yan wasan kwallon kwando na NBA za su zo dakin wasannin domin yin horo.'
Domin samar da kyakkyawar dama ga samari matasa na kasar Sin da na duk duniya wajen cimma kyakkyawan burin wasannin Olympics a kan cewa ' Hadin kai, da zumunci da kuma zaman lafiya', ma'aikatar kula da harkokin bada ilmi ta kasar Sin da kwamitin taron wasannin Olympics na Beijing sun zabi makarantun firamare da na sakandare kimanin 200 na birnin Beijing don su yi cudanya tare da kwamitocin wasannin Olympics na kwamitocin wasannin Olympics na nakasassu da kuma wasu makarantu na sauran kasashe ko jihohi na duniya. Makarantar sakandare ta lamba 8 ta Beijing da Zhang Le ke karatu a ciki ta kulla dangantaka tare da wata makaranta da ake kira ' D'albert' ta kasar Faransa. Da yake Zhang Le ta zama lambawan a fannin karatu a cikin ajinta tare da nuna halin kirki ga kowa, shi ya sa ta yi alfaharin samun damar zuwan kasar Faransa a karo na farko, inda ta koyi harshe, da tarihi da kuma al'adun wannan kasa yayin da take daukar nauyin dake bisa wuyanta na yin bayani kan kasar Sin da kuma taron wasannin Olympics na Beijing ga aminai 'yan kasar Faransa. ( Sani Wang )
|