Yau dai za mu karanto muku wani bayani a game da yadda Malam Zhang Yun daya daga cikin masu masana'antu masu zaman kansu na lardin Sichan na kasar Sin yake zuba jari a kasar Senegal. Abun da ya sosa ran Malam Zhang Yun shi ne ya samu iznin mallakar wani yanki dake cibiyar birnin Dakar, babban birnin kasar Senegal cikin lokacin da bai kai watanni shida ba bayan ya soma bude kasuwar zuba jari a wannan kasa. Yawan kudin da ya zubar ya kai kudin Euro miliyan dari daya da zai yi amfani da shi don kafa wata unguwar tsakiya ta kasuwanci ta zamani.
A ran 19 ga watan da muke ciki, Malam Zhang Yun ya bada goron gayyata ga mai gari Mr. Diopu na Dakar da kuma jakadan kasar Sin a kasar Senegal don su aza tubali ga ginin filin wasannin motsa jiki na gundumar Wakalm na Dakar. Wannan gini na danganta da aikin kafa unguwar kasuwanci ta tsakiya. To, albarkacin ranar bikin aza tubalin, wakilinmu ya ziyarci Malam Zhang Yun, wanda ya furta cewa :
Domin amsa kirarin da shugaba Hu Jintao ya yi a gun taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika a aka gudanar a shekarar da ta shude da kuma kara yin hadin gwiwa tsakanin kasar Sinda kasashen Afrika a fannin tattalin arziki da cinikayya, mun tsaida kudurin zuba jari don kafa wata unguwar kasuwanci ta tsakiya a birnin Dakar. Domin gudanar da wannan aiki, mun rigaya mun samu nasarar sayen kamfanin zuba jari na gine-gine na kasar Senegal, wanda ya samu wani yanki daga gwamnatin kasar a shekarar 2004. Mun yi hayar wannan yanki na tsawon shekaru 50. A lokaci daya, gwamnatin Senegal ta yarda a mika dauwamammen ikon mallakar yankin idan an cimma burinta a fannoni biyu, daya shi ne abun ya zama tilas a raya wannan yanki; na biyu kuma shi ne biya kudin mikawar wannan yanki na dauwamammen lokaci. Bayan da aka yi shawarwari cikin arziki da aminci, aka tsaida kudurin ware kudin mikawar yankin wajen gina gine-gine biyu na wasannin motsa jiki. Filin wasannin motsa jiki na Wakalm yana daya daga cikinsu.
Kazalika, Malam Zhang Yun ya bada karin hasken cewa, unguwar kasuwanci ta tsakiya da za a soma gina ta nan gaba kadan tana a cibiyar birnin Dakar; fadinta ya kai murabba'in-mita 26,000; kuma jimlar fadin ginin ta kai murabba'in-mita 280,000. Wannan babban ginin na da benaye 23, wanda za a kashe kudin Euro miliyan dari daya wajen gina shi.
Sa'annan Malam Zhang Yun ya furta cewa, kyakkyawan matsayin ginin kan taswira da kuma kyakkyawar makoman zuba jari wajen gina shi za su janyo hankulan wasu shahararrun kamfanoni da masana'antu na gida da na waje, da wasu kungiyoyi da kuma hukumomin kudi na kasa da kasa don su zuba jari da gudanar da harkokinsu. A matsayin wani babban gini dake alamanta kasar Senegal, unguwar kasuwanci ta tsakiya ba ma kawai za ta kyautata fuskar duk birnin Dakar ba, har ma za ta bayyana yadda kamfanoni da masana'antun kasar Sin suka amsa kirarin da gwamnatin kasar Sin ta yi na shiga cikin yunkurin bunkasa tattalin arzikin kaashen Afrika. Saboda haka ne dai, gwamnatin wurin da kuma mahukuntan da abin ya shafa suka mai da hankalinsu sosai kan aikin gina unguwar kasuwancin. Shugaba Abdulaye Wade na kasar Senegal shi kansa ne ya amince da gudanar da aikin.
A karshe dai, Malam Zhang Yun ya yi farin ciki da fadin cewa, birnin Dakar, wani muhimmin birni ne dake bakin teku a yammacin Afrika, kuma ya kasance wata muhimmiyar cibiya ce ta musayar kayayyaki da kuma tattalin arziki da cinikayya a wannan shiyya. Muna cike da imanin cewa, matakin gina unguwar da muka dauka zai bude sabon shafi na yunkurin zuba jari da jama'ar kasar Sin suke yi a kasashen Afrika yayin da yake kirkiro sabon salo da za a bi wajen kara yin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a fannin tattalin arziki da cinikayya. ( Sani Wang )
|