Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-19 08:34:30    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (12/09-18/09)

cri

Ran 16 ga wata ne,aka kammala gasar wasan kwallon `croquet` ta makafin duniya na shekarar 2007 da aka shafe kwanaki 4 ana shirya bisa gayyata a birnin Beijing,gasar nan tana cikin jerin gasannin da ake kiransu da suna `Beijing mai sa`a`.A cikin zagaye na karshe na gasar,kungiyar kasar Sin ta lashe kungiyar kasar Sweden ta samu zama ta farko yayin da kungiyar kasar Sweden kuma ta samu zama ta biyu,ban da wannan kuma sai kungiyar kasar Lithuania da kungiyar kasar Amurka sun samu lamba ta uku da ta hudu.Gasar nan ita ce gasa daya kadai da aka shirya musamman domin nakasassu a cikin jerin gasannin `Beijing mai sa`a`.

Ran 16 ga wata ne,aka kammala gasar cin kofin duniya ta wasan tseren mutum daya cikin wasanni 3 na BG na birnin Beijing na shekarar 2007 a tafkin da aka shirya don tanadar ruwa na Shisanling dake karkarar birnin Beijing,a karshe dai,`dan wasa daga kasar Spain Javier Gomez ya samu zama ta farko ta rukunin maza da awa 1 da minti 48 da dakika 41.Shahararriyar `yar wasa daga kasar Portugal Vanessa Fernandes ta samu zama ta farko ta rukunin mata da awa 2 da dakika 35 da 93.

Ran 16 ga wata kuma,an kammala zagaye na karshe na gasar cin kofin duniya ta wasannin zamani iri biyar na shekarar 2007 a birnin Beijing,`yar wasa daga kasar Masar Aya Medany ta samu zama ta farko ta rukunin mata da maki 5536,`yan wasa daga kasar Sin da suka shiga gasar Xiu Xiu da Liu Zhou sun samu lamba ta 19 da ta 35.Kafin wannan kuma,`dan wasa daga kasar Lithuania Edvinas Krungolcas ya samu zama na farko ta rukunin maza da maki 5788,`yan wasa daga kasar Sin Qian Zhenghua da Cao Zhongrong sun samu lamba ta 9 da ta 10.

Ran 16 ga wata ne,an bude gasar cin kofin duniya ta wasan daukan nauyi ta shekarar 2007 a birnin Chiang Mai dake arewacin kasar Thailand.Gasar nan ita ce gasa ta neman samun iznin shiga taron wasannin Olimpic na Beijing,a sabili da haka,`yan wasa 633 da suka zo daga kasashe da shiyoyyi 89 sun zo birnin domin shiga gasar da aka shirya.Za a kammala dukkan gasanni a ran 26 ga wata.

Ran 16 ga wata ne,aka kammala gasar cin kofin duniya ta wasan judo ta shekarar 2007 a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil,kungiyar kasar Japan wadda ta fi karfi a tarihi ta samu lambobin zinariya 3 da na azurfa 2 ta zama zakara,kungiyar kasar Sin ta samu lambobin zinariya 2 ta samu zama ta biyar a cikin jerin sunayen kungiyoyyin da suka samu lambar yabo. (Jamila Zhou)