Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 19:43:27    
Muhimmin tunanin "wakilci a fannoni 3"

cri

Muhimmin tunanin "wakilci a fannoni 3" ma'anarsa ita ce, Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kullum tana wakiltar bukatun bunkasuwar karfin aikin kawo albarka na zamani na kasar Sin, da manufar ci gaba na al'adun ci gaba na kasar Sin, da kuma babbar moriyar tarin jama'ar kasar Sin.

Babban taron wakilan duk kasa na 16 na J.K.S. da aka yi a shekarar 2002 gaba dayansa ya yarda da cewa, za a dauki muhimmin tunanin "wakilci a fannoni 3" tare da Maxanci-Leninanci da Mao Zedong tunani da kuma hasashen Deng Xiaoping a matsayin tunanin jagorancin J.K.S.

Wakiltar bukatun bunkasuwar karfin aikin kawo albarka na zamani na kasar Sin wato dukkan hasashe da tafarkoki da tsare-tsare da ka'idodi da manufofi da kuma ayyuka daban-daban da J.K.S. ke gudanar da su dole ne su yi kokarin dacewa da dokokin bunkasuwar karfin aikin kawo albarka, ta rika daga matsayin zaman rayuwar jama'a ta hanyar bunkasa karfin aikin kawo albarka. Wakiltar manufar ci gaba na al'adun ci gaba na kasar Sin wato dukkan hasashe da tafarkoki da tsare-tsare da ka'idodi da manufofi da kuma ayyuka daban-daban da J.K.S. ke gudanar da su dole ne su yi kokarin biyan bukatun bunkasa al'adun kimiyya na al'umma kuma na jama'a, kuma bisa yunkurawa zuwa manufar zamanintarwa, da zuba ido ga inda duniya ta sa wa gaba, da kuma yin hangen gobe. Wakiltar babbar moriyar tarin jama'ar kasar Sin wato dukkan hasashe da tafarkoki da tsare-tsare da ka'idodi da manufofi da kuma ayyuka daban-daban da J.K.S. ke gudanar da su dole ne su dauki babbar moriyar jama'a a matsayin mafari da makomarsu, ta yadda za a za a rika samar wa jama'a moriyar a zo a gani wajen tattalin arziki da siyasa da al'adu bisa harsashin dinga samun ci gaban zaman al'umma.

Muhimmin tunanin "wakilci a fannoni 3" kuma shi ne sanadin kafa J.K.S. da harsashin tafiyar da mulkinta da kuma mafarin samun karfinta. (Umaru)