Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kafu ne a ran 1 ga watan Yuli na shekarar 1921.
Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kungiyar maduganci ce ta ajin ma'aikata, a sa'i daya kuma kungiyar maduganci ce ta jama'ar kasar Sin da al'ummar kasar Sin, cibiyar shugabanci ce ta sha'anin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin. Tana wakiltar bukatun yalwatuwar karfin aikin kawo albarka na cigaba da manufar cigaba ta al'adu mai cigaba na kasar Sin, tana kuma wakiltar babbar moriyar yawancin jama'ar kasar Sin. Babban buri da makasudin karshe na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin su ne tabbatar da kwaminisanci.
Muhimmin tafarkin da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ke bi a mataki na farko na gurguzu shi ne: Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana jagorantar jama'ar kabilu daban daban na kasar Sin da kuma hada kansu, a waje daya kuma, tana sanya aikin raya tattalin arziki a matsayin cibiyar aiki, haka kuma tana tsayawa tsayin daka kan manyan ka'idoji guda hudu, tana kuma nacewa ga bin manufar bude kofa ga kasashen ketare da yin gyare-gyare, tana yin namijin kokari da kanta kuma tana raya harkokinsu cikin himma da kwazo, ta yadda kasar Sin za ta kasance wata ingantacciyar kasa mai arziki ta zamani kuma mai dimokuradiyya irin ta gurguzu.
Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta dauki Makisanci da Leninanci da Mao Tsedong Tunani da hasashen Deng Xiaoping da muhimmin tunanin wakilci a fannoni 3 a kama da jagorar aikinta. Makisanci da Leninanci sun fito da yadda aka samu bunkasuwar zamantakewar al'ummar mutane, babban tunaninsa gaskiya ne kuma mai kuzari ainun. Ba za a iya cimma babban burin da mabiya jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ke yunkurin binsa ba, sai an tabbatar da tushen raya zamantakewar al'umma irin ta gurguzu sosai a duk fannoni. Yunkurin bunkasa tsarin gurguzu da kuma kyautata shi yana bukatar dogon lokaci cikin tarihi. Ya kamata ta tsaya haikan kan manyan tunanin Makisanci da Leninanci kuma nace ga bin hanyar dake dacewa da halin da kasar Sin ke ciki da jama'ar kasar Sin ta zaba da kanta, ta yadda za a ci nasarar karshe wajen harkokin raya gurguzu a kasar Sin. (Murtala)
|