Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 19:42:04    
Tattara ra'ayoyi ta hanyar demokuradiyya

cri

Wata jam'iyyar siyasa dake da tarihi na tsawon shekaru sama da 80 wadda kuma take rike da mulkin kasar har na tsawon shekaru sama da 50, wata babbar jam'iyya dake da mambobi sama da miliyan 70. Me yasa take kasancewa da rayayyen karfi har kullum? To, wassu kwararru sun yi hasashen cewa, daya daga cikin dalilan da suka sa ta yi haka shi ne domin Jam'iyyar tana nacewa da kuma kyautata tsarin tattara ra'ayoyi ta hanyar demokuradiyya.

Tsarin tattara ra'ayoyi ta hanyar demokuradiyya ya kasance wata muhimmiyar ka'ida da kuma wani tsarin bada jagoranci na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin. Muhimmiyar ma'anar tsarin ita ce, a tattara ra'ayoyi bisa jigon demokuradiyya da kuma shimfida demokuradiyya bisa jagorancin ka'idar tattara ra'ayoyi. A cikin tsarin tattara ra'ayoyi ta hanyar demokuradiyya, shirin shimfida demokuradiyya da na tattara ra'ayoyi suna jibintar juna, wato ke nan shirin demokuradiyya ya kasance sharadin farko da kuma jigo ne na shirin tattara ra'ayoyi; kuma shirin tattara ra'ayoyi ya kasance abin jagoranci da kuma sakamako ne na shirin shimfida demokuradiyya. Nacewa ga bin tsarin tattara ra'ayoyi ta hanyar demokuradiyya na nufin cewa kamata ya yi a sanya matukar kokari wajen kago irin halin siyasa cikin Jam'iyyar, inda ke kasancewa da shirin tattara ra'ayoyi da na shimfida demokuradiyya, da dokokin biyaya da walawa da kuma aniya iri daya da farin ciki na mutum.

" Kundin tsarin ka'ida na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin" ya tanadi muhimmiyar ka'ida a bayyane kan tsarin tattara ra'ayoyi ta hanyar demokuradiyya, wato ke nan wajibi ne 'yan jam'iyyar su bi kungiyar jam'iyyar; mutane kalilan su bi akasarin mutane; kananan hukumomi su bi kungiyoyin da suka yi sama da su; kuma kungiyoyi daban-daban na duk jam'iyyar da kuma dukkan 'yan jam'iyyar su bi babban taron wakilan duk kasa na jam'iyyar da kwamitin tsakiya na jam'iyyar;

Tsarin tattara ra'ayoyi ta hanyar demokuradiyya shi ma tana taka muhimmiyar rawa a cikin zamantakewar kasar Sin. Babban taron wakilan jama'ar duk kasar Sin da babban taron wakilan jama'a na mataki daban-daban na wuraren kasar, akan zabe su ne ta hanyar demokuradiyya, wadanda jama'a suke sa ido kansu.