Bayan yakin `wiwi` da aka yi a shekarar 1840,sai karfin kasar Sin ya ragu kwarai,kuma ta kara talauci,har ta zama wata kasa dake karkashin mulkin mallaka da mulkin gargajiya,wato ta zama wata kasa maras karfi wadda aka yi mata wulakanci kamar yadda ake so.Ya zuwa shekarar 1921,an kafa jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin,wannan shi ne babban al`amari wanda ya kawo babban tasiri ga tarihin zamanin kusa na kasar Sin,daga nan,kasar Sin ta fara yin manyan sauye-sauye.
A karkashin jagorancin jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin,wato bayan gwaggwarmaya mai tsanani da aka yi a cikin shekaru 28 da suka shige,a karshe dai,jama`ar kasar Sin sun kafa sabuwar kasar Sin mai mulkin kansu a shekarar 1949.Kasar Sin ta kammala tarihin wulakancin da aka yi mata na shekaru fiye da dari daya,ana iya cewa kasar Sin ta sami ci gaba mai ma`ana a tarihi.Daga baya kuma,kasar Sin ta fara yin gyare-gyare kuma ta fara aiwatar da manufar bude wa kasashen waje kofa a karkashin jagorancin jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin.Yanzu dai an riga an tabbatar da wadatuwa a kasar Sin kuma jama`ar kasar Sin suna kara samun wadatuwa a kan hanyar gurguzu mai tsarin musamman na kasar Sin,haka kuma karfin aikin kawo albarka na zamantakewar al`umma da hadadden karfin kasa da matsayin zaman rayuwar jama`ar kasar Sin sun dada daguwa a bayyane.Yanzu,a karkashin jagorancin jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin,jama`ar kasar Sin suna yin kokarin fama da manyan sauye-sauyen dake cikin gida da na duniya,kuma kasar Sin mai tsarin gurguzu tana kara karfi a dandalin duniya.
Kafuwar jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin da bunkasuwarta sun canja tarihin kunya na kasar Sin,kuma sun sa kasar Sin ta sake zama wata kasa mai karfi a duniya.A kasar Sin,akwai wata waka dake yaduwa sosai,wakar nan ana rera ta kamar haka:`In babu jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin,to da babu sabuwar kasar Sin,jami`yyar kwaminis ta kasar Sin ta yi kokari domin kara wadatuwar al`ummar kasar Sin,jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi kokari domin ceton kasar Sin??`(Jamila Zhou)
|