Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 19:41:22    
Ra'ayin samun bunkasuwa ta hanyar kimiyya

cri

Abin da ake nufi da ra'ayin samun bunkasuwa ta hanyar kimiyya shi ne nacewa ga ra'ayin mayar da moriyar jama'a a gaban kome, yayin da ake neman samun bunkasuwa mai dorewa cikin daidaituwa kuma a duk fannoni.

An gabatar da wannan ra'ayi ne a gun cikakken zama na 3 na kwamitin tsakiya na 16 na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da aka yi a shekarar 2003. Ra'ayin ya jaddada cewa, bisa bukatun da ake yi wajen gudanar da hadadden tsari tare da yin la'akari da ko wane bangare don raya birane da kauyuka da tatttalin arziki da zamantakewar al'umma da tabbatar da zaman jituwa a tsakanin dan adam da halitta, da kuma raya kasa da bude wa kasashen waje kofa, a ciyar da harkokin gyare-gyare da ci gaban kasar Sin gaba.

Abin da ake nufi da mayar da moriyar jama'a a gaban kome shi ne, ya kamata a dauki moriyar jama'a bisa matsayin babbar manufar duk ayyuka, a yi ta biya bukatun da jama'a ke yi a fannoni da yawa, sa'an nan a ciyar da ci gaban dan adam gaba a duk fannoni.

Abin da ake nufi da ciyar da ci gaban dan adam gaba a duk fannoni, shi ne yayin da ake ta kyautata tsarin tattalin arziki na kasuwanni na gurguzu, da samun ci gaba mai dorewa wajen bunkasa tattalin arziki cikin sauri da daidaituwa, ya kamata, a gaggauta samun wayewar kai a fannonin siyasa da na al'adu, ta yadda za a kafa tsarin taimakon juna da samun bunkasuwa tare ta hanyar samun wayin kai a fannonin kayayyaki da siyasa da al'adu; abin da ake nufi da samun bunkasuwa cikin daidaituwa shi ne, ya kamata, a gudanar da hadadden tsari tare da yin la'akari da ko wane bangare don raya birane da kauyuka cikin daidaituwa, da raya shiyya-shiyya cikin daidaituwa, da bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma cikin daidaituwa da raya kasa da bude wa kasashen waje kofa; abin da ake nufi da samun ci gaba mai dorewa shi ne, ya kamata, a gudanar da hadadden tsari tare da yin la'akari da ko wane bangare don samun ci gaban dan adam da halitta kamar yadda ya kamata, da daidaita huldar bunkasuwar tattalin arziki da karuwar yawan mutane da yin amfani da albarkatun kasa da kiyaye lafiyar yanayin kasa, da sa kaimi ga duk zamantakewar al'umma da ta bi hanyar samun bunkasuwa cikin wayin kai tare da samun bunkasuwar aikin samar da kayayyaki da zaman wadata da lafiyar yanayin kasa.

Ra'ayin samun bunkasuwa ta hanyar kimiyya tunani ne mai muhimmanci da Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta gabatar bisa manyan tsare-tsare da babbar manufar raya kasar Sin a sabon lokaci na karni na 21. (Halilu)