Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 19:40:37    
Zamantakewa da duniya masu daidaituwa

cri

"Zamantakewa mai daidaituwa" tana nufin a kafa wata zamantakewa mai bin tsarin demakuradiya da dokoki, da tsayawa kan daidaici da adalci, da amincewa da kauna, da cike da kuzari, zaman kwanciyar hankali da odar da samun jituwa tsakanin Bil Adam da halittu a kasar Sin.

An gabatar da wannan ra'ayin "zamantakewa mai daidaituwa " ne a gun cikakken zama na hudu na kwamitin tsakiya na 16 na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da aka yi a shekara ta 2004. Haka kuma wata muhimmiyar dawainiyya ce da Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta gabatar tare da zumar gina wata zamantakewa mai dadi daga dukkan fannoni da bude wani sabon yanayi kan sha'anin gurguzu mai halayen musamman na kasar Sin, ta shaida muhimmiyar moriya da burin dimbin mutanen kasar Sin.

"Duniya mai daidaituwa" tana nufin cewa yayin da kasar Sin ta daidaita huldodin dake tsakanin kasa da kasa, ta tsaya ga bin ra'ayin bangarori da dama da tabbatar da tsaron tarayya, ta nace ga bin ka'idar hadin kan moriyar juna da samun wadatuwa tare, da ta nace ga yin hakuri da kafa duniya mai daidaituwa. Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gabatar da wannan ra'ayi da farko a taron koli na tunawa da cikon shekaru 60 da kafa majalisar dinkin duniya a shekara ta 2005. Ra'ayin nan ya hada burin kasar Sin wajen harkokin waje da abun da ke muhimmin shirinta na game da duniya.

A cikin shekarun baya, shimfida zamantakewa da duniya masu daidaituwa sun zama muhimman ka'idoji da kasar Sin take bi wajen raya kasa cikinlumana. Ci gaba da wadatuwar duniya na bukatar ci gaban kasar Sin mai daidaituwa, Ci gaba da wadatuwar kasar Sin ba ya iya rabuwa da duniyar dake samun ci gaba mai daidaituwa."zamantakewa mai daidaituwa"da "duniya mai daidaituwa"suna bukatar juna da taimakon juna.Kasar Sin ta dukufa wjen shimfida zamantakewa mai daidaituwa, babu shakka ta ba da sabon tamako ga yunkurin shimfida duniya mai daidaituwa,yunkurin da kasar Sin ta yi wajen mayar da duniya ta zama mai daidaituwa, babu shakka ya kawo wani yanayin duniya mai amfani ga kasar Sin wajen shimfida zamantakewa mai daidaituwa.(Ali)