Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 19:40:18    
Tarurrukan wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin a wurare na matakai daban daban

cri

Jam'iyyar kwaminis ta Sin ta kafa rassanta a larduna da birane da kuma gundumomi daban daban na kasar. Hukumomin da ke jagorancin wadannan rassan jam'iyyar su ne tarurrukan wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin a wurare na matakai daban daban da kuma kwamitoci na matakai daban daban da suka haifar. A kan zabi wakilan tarurrukan ne daga 'yan jam'iyyar kwaminis ta Sin da ke a wurare daban daban. Sa'an nan, a kan gudanar da tarurrukan a shekaru biyar biyar. Tarurrukan da kuma kwamitocin da suka haifar suna daukar nauyin aiwatar da manufofin da rassan jam'iyyar kwaminis ta Sin da ke shugabancinsu suka bayar, tare kuma da ba da jagoranci a kan ayyukan da ake gudanarwa a wurare daban daban.

Hakkokin da tarurrukan suke da su sun hada da: sauraron rahotannin kwamitocin jam'iyyar kwaminis ta Sin da ke cikin mataki daya da kuma yin bincike a kansu, da sauraron rahotannin kwamitocin ladabtarwa da ke cikin mataki daya da su da kuma yin bincike a kansu, da tattauna manyan al'amura na yankunansu tare kuma da yanke shawara a kansu, da zaben kwamitocin jam'iyyar kwaminis ta Sin da ke cikin mataki daya da su da kuma kwamitocin ladabtarwa na jam'iyyar wadanda kuma ke cikin mataki daya da su.(Lubabatu)