Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 19:39:55    
Hasashen Deng Xiaoping

cri

Hasashen Deng Xiaoping shi ne takaitaccen sunan "hasashen Deng Xiaoping dangane da raya zaman gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin".

A sabon lokacin tarihin raya zaman gurguzu a kasar Sin, kuma cikin sabuwar aikatawar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, 'yan J.K.S wadanda Mr. Deng Xiaoping ke alamanta su sun fara samun wata hanyar raya zaman gurguzu wadda ta dace da sigar kasar Sin, kuma sun sami manyan nasarori wajen yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje da raya zaman gurguzu na zamani bisa harsashin tattara fasahohi daga abubuwa masu kyau da marasa kyau wajen raya zaman gurguzu tun bayan kafa sabuwar kasar Sin, kuma bisa harsashin bincika fasahohin kasashen duniya da al'amuran duniya. Sakamakon hasashen da aka samu cikin wannan lokacin tarihi wanda ya samu tabbatuwa ta hanyar aikatawa cewa, shi ne hasashen zaman gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin wanda zai iya ba da jagoranci ga samun nasarar raya kasar Sin mai mulkin gurguzu kuma daidai da zamani, wannan shi ne hasashen Deng Xiaoping.

Hasashen Deng Xiaoping ya tsaya kan tafarkin tunani na 'yanta da tunani da nuna gaskiya daga abubuwan hakika, karo na farko kuma cikin tsari ne ya ba da amsa ga tambayar cewa, "Mene ne zaman gurguzu?" kuma "Ta yaya za a raya zaman gurguzu" a irin kasa mai rishin ci gaba wajen tattalin arziki da al'adu kamar kasar Sin? da sauran muhimman tambayoyi a jere. Ya arzuta da kuma gaji Maxanci-Leninanci da Mao Zedong tunani, shi ne Maxanci na kasar Sin ta zamani, kuma shi ne sabon matakin ci gaban Maxanci a kasar Sin.

Hasashen Deng Xiaoping shi ne tattarawar fasahohin aikatawa da hikimar tarayya na jama'ar kasar Sin, kuma shi ne jagorar ayyukan 'yan J.K.S. wajen raya zaman gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin.

Mr. Deng Xiaoping wanda ya yi zamansa a duniya daga shekarar 1904 zuwa ta 1997, shi ne babban mutum dake cikin kungiyar shugabanci ta zuriya ta 2 ta sabuwar kasar Sin, wanda kuma ake kiran shi da sunan babban mai tsara fasalin harkokin kasar Sin wajen yin gyarye-gyare da bude kofa ga kasashen waje. (Umaru)