Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 19:39:05    
Bauta wa Jama'a

cri

Wakiltar ainihin moriyar dukkan jama'ar kasar da bauta wa jama'a da zuciya daya aihinin tushe ne ga kasancewar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Bauta wa jama'a shi ma kwayar tunanin zaman rayuwa da tunanin ladabi da da'a na tsarin gurguzu na kasar Sin.

Mao Tsetong wanda yake daya daga cikin shugabannin kafa jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da Jamhuriyar Jama'ar Sin ya taba bayyana cewa, "muhimmin bambancin da ke kasancewa a tsakanin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da sauran jam'iyyun siyasa shi ne, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana kokarin hada kanta da dukkan jama'ar kasar, kuma tana kokarin bauta wa jama'a da zuciya daya. Ba ta son a ware ta da jama'a a kowane lokaci. Tana kuma aiwatar da harkoki domin moriyar jama'a, amma ba moriyar wani mutum ko wata kungiya kawai ba."

A shekarar da muke ciki, Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya sake jaddada cewa, "ainihin burin da jam'iyyarmu take kokarin cimmawa shi ne bauta wa jama'a da zuciya daya. Jam'iyyarmu tana gwagwarmaya da yin aiki ne domin kawo wa jama'a alheri. Dole ne mu sa dukkan aikace-aikacen tabbatar da kiyayewa da kara neman cimman ainihin moriyar jama'a a kan matsayin dalilan da jam'iyyarmu da gwamnatinmu suke yin aikinsu da buri ne da suke son cimmawa. Dole ne mu gane cewa muna neman bunkasuwa domin jama'a, muna dogara da jama'a wajen neman bunkasuwa, jama'a ne suke more sakamakon cigaban da muke samu."

A waje daya, bauta wa jama'a kwayar tunanin zaman al'ummar gurguzu na kasar Sin. A cikin zaman rayuwar yau da kullum, bauta wa jama'a yana almanta cewa, lokacin da ake yin wani abu, ya kamata a mai da hankali kan moriyar sauran mutane, kuma a yi kokarin moriyar sauran mutane da zaman al'ummarmu. Kuma ya kamata a yi kokarin mayar da abubuwan da ake yi da ya zama kyakkyawan sakamako ga sauran mutane da zaman al'ummarmu. (Sanusi Chen)