Lardunan Shanxi da Anhui da Henan da Jiangxi da Hunan da kuma Hubei suna tsakiyar kasar Sin, kuma su kyawawan mahada ne wajen hada yankunan da ke gabashi da kuma yammacin kasar Sin tare, da kuma hada yankunan da ke kudanci da arewacin kasar tare. Yawan mutanen lardunan shida ya kai 28 cikin dari bisa dukkan yawan mutanen kasar Sin, kuma jimlar kudaden da suka samu wajen tattalin arziki ta kai fiye da kashi 20 cikin dari bisa na dukkan kasar. Wadannan larduna shida su muhimman yankuna ne wajen samar da amfanin gona, ban da wannan kuma su cibiyoyi ne wajen zirga-zirgar kasar Sin, kuma muhimman wurare ne na makamashi da kuma danyun kayayyaki, sabo da haka suna taka muhimmiyar rawa ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Sin bisa manyan tsare-tsare.
Sa kaimi ga farfadowar yankunan tsakiyar kasar Sin wata muhimmiyar manufa ce daban da kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da kuma majalisar gudanarwa ta kasar suka tsara bayan aiwatarwar manufofin kara kwarin gwiwar gabashin kasar Sin wajen samun bunkasuwa da farko, da raya yammacin kasar, da kuma farfado da arewa maso gabashin kasar da dai sauran tsoffin sansanonin masana'antu, kuma wani muhimmin aiki ne wajen aiwatar da babban tsarin sa kaimi ga samun bunkasuwar kasar Sin gaba daya cikin daidaito.
Samun farfadowar tsakiyar kasar Sin yana da muhimmiyar ma'ana ga samun sabon tsari na tuntubar gabashi da tsakiya da kuma yammacin kasar, da taimaka wa juna, da sa kaimi ga juna don samun bunkasuwa gaba daya. A 'yan shekarun nan da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan sa kaimi ga farfadowar yankunan tsakiyar kasar. Shiri na 11 na bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin cikin shekaru 5 masu zuwa ya nuna cewa, ya kamata tsakiyar kasar Sin ta dogara bisa karfinta na yanzu, da kyautata matsayin sana'o'i, da kuma sa kaimi ga karuwar masana'antu da birane, ta yadda za ta iya samun farfadowa wajen hada yankunan da ke gabashin da yammacin kasar Sin tare da nuna fifiko wajen bunkasa sana'o'i.
|