Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 19:38:07    
Farfado da yankunan arewa maso gabashin kasar Sin

cri

Yankin lardunan Heilongjiang da Jilin da kuma Liaoning da ke arewa maso gabashin kasar Sin ya kasance tamkar wani gadon jinjiri ne na bunkasa masana'antun sabuwar kasar Sin, sun ba da babban taimako wajen kafa cikakken tsarin masana'antu masu zaman kansu na kasar Sin, da tsarin tattalin arzikin kasar. Amma, sabo da tun tuni aka kafa tsofaffin wuraren da ake da masana'antu dake yankin arewa maso gabashin kasar, kuma a cikin dogon lokaci ne sansanin ya kasance cikin yanayi maras kyau da tsari ya kawo, bugu da kari kuma wasu masana'antu sun shiga yanayin lalacewa, har ma sun rasa karfin takara. Musamman ma wasu biranen da ke dogara da hako ma'adinai domin raya wasu masana'antu, sun gamu da babbar matsala. A sakamakon haka, ya kasance da gibi ainnu a tsakanin tsofaffin wuraren da ake da masana'antu dake yankin arewa maso gabashin kasar, da kuma yankuna masu ci gaba da ke gabar teku a fannin bunkasuwar tattalin arziki.

Kan wadannan batutuwa, a gun babban taron wakilan duk kasar Sin a karo na 16 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da aka shirya a shekarar 2002, an gabatar da cewa, "za a tallafawa tsofaffin wuraren da ake da masana'antu dake yankin arewa maso gabashin Sin da sauran larduna a matsayin yunkurin gaggauta yin garambawul a fannin fasaha, da kuma bayar da kwarin guiwa ga birane ko yankuna wadanda suke dogaro da hako ma'adinai domin raya tsohuwar sana'a", an tsaida kudurin daidaitawa da gyara da kuma farfado da tsohon sansanin masana'antu da ke arewa maso gabashin kasar.

Yanzu, wasu matsakaita da manyan kamfannoni na gwamnatin kasar Sin da ke arewa maso gabashin kasar sun kammala gyare-gyare a jere a fannonin sake tsarin kadarorin kamfannoni, da kuma hada-hadar kudi, da dai sauransu. Wasu birane ko yankuna wadanda suke dogaro da hako ma'adinai domin raya wasu masana'antu kuma sun samu bunkasuwa bisa mataki na farko wajen sauya samfurorin sana'a, da kammala aikin bunkasa tsohuwar sana'a, an fara canza halin koma baya wajen tattalin arziki cikin dogon lokaci a duk yankunnan, har ma an samu bunkasuwa. (Bilkisu)