Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 19:37:43    
Taruruka mafiya ma`ana a tarihin jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin

cri

A tarihin jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin,taruruka mafiya ma`ana sun hada da `taron da aka yi a ran 7 ga watan Agusta` da `taron Zunyi` da kuma `cikakken taro na 3 na zama na 11 na kwamitin tsakiya na jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin`.

A shekarar 1927,saboda jam`iyyar GMT ta wancen lokaci ta ci amanar juyin-juya-hali ta yi kashe-kashe ga `yan jam`iyyar kwaminis ,a sanadiyar haka,yakin juyin-juya-hali na farko dake cikin gida na kasar Sin ya bi ruwa.A ran 7 ga watan Agusta na wannan shekara,kwamitin tsakiya na jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin ya kira wani taro cikin gaggawa a birnin Hankou na jihar Hubei ta kasar Sin,ana kiran wannan taro da sunan `taron ran 7 ga watan Agusta`.A gun taron da aka yi,an kawar da manufar tsattsauran ra`ayi wato manufar ba da kai da aka bi,kuma an kafa sabuwar babbar manufa ta jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin wato yin juyin-juya-hali a karkara da kuma yaki da manufar kashe-kashe ta jam`iyyar GMT.Taron ya samar da sabon izni ga jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin wadda ke cikin halin rudani,ana iya cewa,taron ya ba da babbar gudumuwa wajen ceton jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin da juyin-juya-hali na kasar Sin.

A watan Oktoba na shekarar 1934,a karkashin jagorancin manufar tsattauran ra`ayi na Wang Ming,sojojin jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin sun ga tilas ne su yi maci na dogon zango.A kan hanyar maci,wato a watan Janairu na shekarar 1935,hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi taron yawaita wakilai a birnin Zunyi na jihar Guizhou.A gun taron,an kammala mulkin tsattsauran ra`ayi a kwamitin tsakiya na jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin,kuma an kafa matsayin jagoranci na Mao Zedong a rundunar sojoji da kuma kwamitin tsakiya na jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin.Taron Zunyi yana da babbar ma`ana a tarihin jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin.

A watan Disamba na shekarar 1978,an yi cikakken taro na 3 na zama na 11 na kwamitin tsakiya na jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin a birnin Beijing,babban birnin kasar Sin.A gun taron nan,an sake kafa ka`idar tunani wato `yantar da tunani da kuma nuna halin neman gaskiya daga hakikanin abu.Ban da wannan kuma,an tsai da cewa,za a mai da hankali kan aikin gine-ginen zamani na gurguzu,kuma za a fara yin gyare-gyare a duk fadin kasa kuma za a bude kofa ga kasashen waje.Kazalika,an sake kafa manufar jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin mai dacewa,kuma an tsai da cewa,za a kara kyautata tsarin jam`iyyar da kuma kyautata dokoki da ka`idoji na jam`iyyar.Taron ya warware manyan matsaloli a jere da ba a warware su ba a tarihi.Ban da wannan kuma,a gun taron,an yi sharhi kan ayyukan wasu mihimman shugabannin kasar Sin.

Ana iya cewa,taron nan ya soke tasirin da tsattsauran ra`ayi na kuskure ya kawo wa kasar Sin cikin dogon lokaci wato tun bayan da aka kafa sabuwar kasar Sin a shekarar 1949 daga dukkan fannoni,kuma ya gyara tunanin jagoranci na jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin wato ya sake kafa ka`idar Marksanci ta jam`iyyar,daga nan an bude wani sabon shafi a tarihin jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin da sabuwar kasar Sin.Ko shakka babu,yana da ma`ana mai zurfi a tarihin jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin.(Jamila Zhou)