Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 19:37:12    
Raya kauyuka na sabon salo

cri

Raya kauyuka na sabon salo na gurguzu Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta gabatar da wannan ne a gun cikakken zaman taronta na biyar na kwamitin tsakiya na 16, makasudinsa shi ne domin raya kauyukan kasar Sin da su zama zamantakewar al'umma "mai bunkasuwar aikin samar da kayayyaki da zaman wadata da wayayyen kai da tsabta da kuma kulawa da harkoki cikin dimokuradiyya".

Manyan fannonin raya sabbin kauyuka na gurguzu su ne, na daya raya tattalin arzikin kauyuka, da kara wa manoma kudin shiga; na biyu gina kananan garuruwa da kauyuka da kyau, da kyautata muhallin kauyuka; na uku bunkasa sha'anonin jin dadin jama'ar kauyuka, da sa kaimi ga tabbatar da jituwar zamantakewar al'umma; na hudu horar da manoma da kara daga matsayin kwarewarsu.

Haka kuma sauran abubuwa da suka shafi harkokin raya kauyuka na sabon salo na gurguzu sun hada da kara raya kyawawan al'adu a kauyuka, da gabatar da kyawawan halaye masu wayin kai da kuma nuna su ga zamatakewar al'ummar kauyuka, da raya gine-ginen al'adu a kauyuka, da kyautata zaman rayuwar manoma a fannin al'adu, da inganta kungiyoyin masu ikon kai na matakin kauyuka, da kuma jagorantar manoma wajen shiga aikin raya kauyuka kamar yadda ya kamata kuma bisa burinsu.

Raya sabbin kauyuka na gurguzu sun shafi fannonin kauyuka da yawa kamar na tattalin arziki da siyasa da al'adu da ba da ilmi da kiwon lafiya da kiyaye muhalli da sauransu, abubuwansa suna da yawa, kuma yana da ma'ana mai zurfi, haka kuma wannan tsarin ka'idojin aiki ne ga harkoki da ake yi domin aikin noma da kauyuka da manoma a kasar Sin ta zamani. (Halilu)