Kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya gabatar da shirin raya yammacin kasar Sin a shekarar 1999, domin gaggauta bunkasa yammacin kasar. Wannan ne kasaitaccen shirin da ba a taba gani irinsa ba a tarihin dan Adam.
Shirin raya yammacin kasar ya shafi jihohi da larduna da kuma birane 12, ciki har da birnin Chongqing, da lardin Sichuan, da lardin Guizhou, da lardin Yunnan, da jihar Tibet, da jihar Mongoliya ta gida, da kuma jihar Guangxi, da dai sauransu, fadinsu ya kai murabba'in kilomita miliyan 6.85, wanda ya dau kashi 71.4 cikin dari bisa na duk kasar, yawan mutanensu kuma ya kai kusan biliyan 0.4. A yammacin kasar Sin da akwai azurtattun albarkatun kasa duk da haka a baya yake wajen samun bunkasuwa, bisa wasu dalilan halittu, da tarihi, da kuma zaman takewar al'umma. Yawancin mutane masu fama da talauci na kasar Sin suna zama a yammacin kasar ne.
Babban makasudi na shirin raya yammacin kasar Sin shi ne, ya zuwa tsakiyar karni na 21, wato lokacin da ake cim ma burin mayar da kasar Sin ta zamani a duk kasar a takaice, za a canza halin koma baya da yammacin kasar ke ciki, kazalika za a rage bambanci da ke tsakanin bangarori, bugu da kari kuma za a yi kokarin kafa sabon yammacin kasar Sin mai wadatuwa wajen tattalin arziki, da samun ci gaban zaman takewar al'umma, da zaman kwanciyar hankali, da hadin gwiwar kabilu daban daban, da kayatarwa, da kuma jama'a masu wadata.
Tun bayan da aka soma aiwatar da wannan shiri, gwamnatin kasar Sin ta ba da karin taimako ga yankunan yammacin kasar a fannonin ba da jagora wajen tsara shiri, da nuna goyon baya wajen manufofi, da zuba jari, da shirin ayyuka, da yin musayar kwararru, da dai sauransu. Ya zuwa karshen shekarar 2005, jimlar kudin da gwamnatin kasar Sin ta zuba kan shirin ta kai kudin Sin yuan biliyan 1600, yawan kudin da aka samu daga wajen samar da kayayyaki a yankunan yammacin kasar Sin ya karu da kashi 10.6 cikin dari a ko wace shekara, yawan kudin shiga da wurarre daban daban suka samu ya karu da kashi 15.7 cikin dari a ko wace shekara. Sabbin manyan gine-gine da aka yi sun wuce 70. Tattalin arziki na yankunan yammacin kasar yana ta samun bunkasuwa, kuma an samu kyautatuwa sosai wajen kiyaye muhalli, da manyan ayyuka. (Bilkisu)
|