Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 19:35:51    
Raya birane da kauyuka bisa tsarin bai daya

cri

Huldar da ke tsakanin birane da kauyuka a kasar Sin ita ce hulda mai muhimmanci a cikin tsarin raya tattalin arzikin kasa da zamantakewar al'umma. Yanzu, ya kasance da babbar rata a bayyane a tsakanin birane da kauyuka na kasar Sin wajen raya tattalin arziki da samar wa mazauna kudin shiga da matsayin saye da sayarwa. Game da batun, a gun babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da aka kira a shekarar 2002, jam'iyyar ta bayyana a bayyane cewa, ya kamata a kafa zamantakewar al'umma mai dan wadata tare da cin gashin kanta, a kai a kai ne za a jure halin da ake ciki na kara ratar da ke tsakanin ma'aikatan masana'antu da manoma da kuma tsakanin birane da kauyuka da kuma tsakanin wuri da wuri. A gun cikakken taro na uku na kwamitin tsakiya na 16 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, jam'iyyar ta kara gabatar da bukatun aiwatar da tsarin bai daya a fannoni 5 , na farko shi ne aiwatar da tsarin bai daya wajen raya birane da kauyuka.

Aiwatar da tsarin bai daya wajen raya birane da kauyuka, shi ne don tsara fasali bisa tsarin bai daya wajen raya tattalin arzikin birane da kauyuka da zamantakewar al'umma, a yi la'akari da ayyuka daga dukkan fannoni, wato a yi bincike sosai daga dukkan fannoni a kan batutuwan da suke kasancewa a birane da kauyuka da kuma huldar da ke tsakaninsu, sa'anan kuma za a daidaita su bisa tsarin bai daya. Hakikanin abun da za a yi na raya birane da kauyuka bisa tsarin bai daya shi ne don kafa tsari na taimaka wa juna a tsakanin birane da kauyuka tare da samun ci gabansu gaba daya ta hanyar hada masana'antun birane da na kauyuka da kawar da tsari na matakai biyu a tsakanin birane da kauyuka da kuma kara karfin ingizawa na birane da garuruka don ba da jagoranci ga kauyuka. Aiwatar da tsarin bai daya wajen raya birane da kauyuka shi ne don cim ma buri mai wajabci na samun bunkasuwa mai dolewa a dukkan fannoni bisa daidaici, haka kuma bukata ce da ake yi dole don nacewa ga samun bunkasuwar 'yan adam daga dukkan fannoni bisa tsarin mayar da 'yan Adam bisa matsayi mai muhimmanci sosai. Sa'anan kuma abu ne mai muhimmanci wajen aiwatar da ra'ayin raya kasa bisa kimiyya.(Halima)