Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kira babban taro na dukkan wakilanta na 16 a shekarar 2002. Sa'anan kuma, cikakken taro na kwamitin tsakiya na jam'iyyar ta gabatar da manufofi da matakai wadanda muhimmansu suka hada da batun aiwatar da ra'ayin raya kasa bisa kimiyya da kara inganta ayyukan kara karfin jam'iyyar wajen aiwatar da harkokin mulki da kafa zamantakewar al'umma mai mulkin gurguzu kuma mai jituwa da sauransu.
Takardun da abin ya shafa kuma cikakken taro na biyu na kwamitin tsakiya na 16 na jam'iyyar ya bayar sun karfafa cewa, ya kamata a sauya ayyukan gwamnati da kuma kyautata hanyoyin aiwatar da harkokinta da kuma gyara halayyen aiki da kara samun sakamako daga wajen ayyukan hukumomi, sa'anan kuma a yi kokarin kafa tsarin aiwatar da harkokin hukumomi bisa tsari da daidaituwa da adalci kuma a bayyane ba tare da cin hanci da rashawa ba.
Cikakken taro na uku na kwamitin tsakiya na 16 na jam'iyyar a bayyane ne ya gabatar da ra'ayi na nacewa ga mayar da 'yan adam bisa matsayi mai muhimmanci sosai da samun bunkasuwa mai dorewa bisa daidaici a dukan fannoni da sa kaimi ga raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma da 'yan adam daga dukan fannoni. Wannan ne ra'ayin raya kasa bisa kimiyya da jam'iyyar ta gabatar a karo na farko a cikin takardar da ta bayar. Taron ya kuma gabatar da cewa, kyautata tsarin tattalin arziki na kasuwanci na mulkin gurguzu ya kamata a aiwatar da tsarin bai daya a fannoni biyar da kuma nacewa ga cim ma buri a fannoni biyar, wato, aiwatar da tsarin bai daya wajen raya birane da kauyuka da kuma aiwatar da tsarin bai daya wajen raya shiyya da shiyya da aiwatar da tsarin bai daya wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma da aiwatar da tsarin bai daya wajen raya 'yan adam da halittu cikin jituwa da aiwatar da tsarin bai daya wajen samun bunkasuwa a cikin gida da biyan bukatun da ake yi wajen bude kofa ga kasashen waje; Ya kamata a nace ga bin manufar yin gyare-gyare kan tattalin arziki na kasuwanci na mulkin gurguzu da kuma nacewa ga girmama jama'a wajen kago sabbin kayayyaki da nacewa ga daidaita huldar da ke tsakanin gyare-gyare da samun bunkasuwa da zaman karko yadda ya kamata da kuma nacewa ga aiwatar da tsarin bai daya daga dukan fannoni da kuma mayar da 'yan adam bisa matsayi mai muhimmanci.
Cikakken taro na hudu na kwamitin tsakiya na 16 na jam'iyyar ya tsai da kuduri na mayar da abu mai muhimmanci na raya jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin bisa matsayin karfinta na aiwatar da harkokin mulki, ya karfafa cewa, ya kamata a kara karfafa muhimmanci ga karfin jam'iyyar wajen aiwatar da harkokin mulki cikin gaggawa, ya gabatar da cewa, ya kamata a aiwatar da harkokin mulki ta hanyar kimiyya da dimokuradiya da dokokin shari'a.
Cikakken taro na 5 na kwamitin tsakiya na 16 na jam'iyyar ta tsai da kuma ta bayyana babban fasali mai girma na kasar Sin wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma a sabon karni bisa shirin raya kasa na biyu na shekaru biyar biyar, ya gabatar da cewa, a cikin lokacin aiwatar da shirin raya kasa na 11 na shekaru biyar biyar, dole ne a kiyaye halin da ake ciki na raya tattalin arziki a kai a kai kuma da sauri, dole ne a kara saurin sauya hanyar kara karuwar tattalin arziki da kuma dole ne a dogara bisa karfinsu na kansu wajen kara karfin yin kirkire-kirkire , dole ne a sa kaimi ga raya birane da kauyuka bisa daidaici, dole ne a kara inganta ayyukan kafa zamantakear al'umma mai jituwa kuma dole ne a kara zurfafa gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje.
Cikakken zama na 6 na kwamitin tsakiya na 16 na jam'iiyar ta tsai da kuduri cewa, a nan gaba, kasar Sin za ta mayar da aikin kafa zamantakewar al'umma mai jituwa bisa matsayi mai muhimmanci sosai. Ya zuwa shekarar 2020, manufar kafa zamantakewar al'umma mai jituwa kuma mai mulkin gurguzu ita ce, kara kyautata dimokuradiya da dokokin shari'a, ana kara ba da tabbaci ga jama'a wajen samun ikonsu da fa'idarsu da girmamawa ta hakika. Halin da ake ciki na kara ratar da ke tsakanin birane da kauyuka da shiyya shiyya zai sauya a kai a kai, za a kuma kafa tsarin raba kudin shiga bisa adalci kuma bisa ka'ida, za a kuma kara biyan bukatun da aka yi na samun aikin yi a zamantakewar al'umma , za a kuma kafa tsarin ba da tabbaci ga taimaka wa jama'a, sa'anan kuma za a kara kyautata tsarin samar da hidima ga jama'a, kuma matsayin gwamnati wajen samar da hidima da aiwatar da harkokinta zai kara daguwa, tunanin duk al'umma da da'ar da suke bi da kuma al'adu da kimiyya da suke samuwa da lafiyarsu sai kara daguwa a bayyane suke yi, hakan kuma an riga an kafa hulda mai jituwa da ke tsakanin 'Yan adam , An kuma kafa kasar da ke iya kirkire-kirkire, tsarin aiwatar da harkokin zamantakewar al'umma sai kara samun kyautatuwa, odar zamantakewar al'umma ita ma ta kara kyau, muhallin halittu kuma ya sami sauyawa kuma ya yi kyau sosai da sauransu. (Halima)
|