Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 19:34:38    
Hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya ta Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin

cri

Hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya ta Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin cibiya ce ta hukumomin ba da jagoranci na kwamitin tsakiya na jam'iyyar. A watan Afril na shekara ta 1927, JKS ta kafa hukumar a gun babban taro na karo na biyar na wakilan 'yan jam'iyyar na duk fadin kasar.

An samu hukumar ne ta hanyar yin zabe a gun cikakken taron kwamitin tsakiya na JKS. Bisa abubuwan da aka tanada a cikin kundin tsarin jam'iyyar da aka bayar a gun babban taro na karo na 12 na wakilan 'yan Jam'iyyar, an ce, hukumar siyasa ta jam'iyyar ita ce ta shirya cikakken taron kwamitin tsakiya na jam'iyyar a kalla sau daya a ko wace shekara. Hukumar siyasa ta jam'iyyar da kuma zaunannen kwamitinta suna gudanar da ikon kwamitin tsakiya na JKS lokacin da ba a yi cikakken taro ba. Haka kuma ya kamata hukumar siyasa ta jam'iyyar ta bayar da rahotannin aiki ga kwamitin tsakiya na jam'iyyar na bisa kayadadden lokaci.

Hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS tana bin ka'idar jagorancin hadin gwiwa, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar shi ne yake kula da aikin kiran taron hukumar siyasa. Dole ne hukumar ta bi tafarku da ka'idoji da manufofin da babban taron wakilan JKS na duk fadin kasar Sin ya zartar a tsanake. Kuma dole ne kudurorin da hukumar ta tsayar kan sake wuraren ayyukan 'yan hukumar ba da jagoranci ta kwamitin tsakiya na JKS da kuma muhimman al'amuran da ke cikin jam'iyyar sun samu amincewa daga cikakken taron kwamitin tsakiya na JKS.