Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 19:34:15    
Jam'iyyun dimokuradiya na kasar Sin

cri

Jam'iyyun dimokuradiya na kasar Sin su ne, a duk fadin babban yankin kasar Sin, ban da Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da ke kan ragamar mulki, sauran jam'iyyu guda takwas da ke shiga cikin harkokin siyasa, wadanda suka hada da kwamitin juyin juya hali na Jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin, wanda rukunin dimokuradiya na Jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin da sauran mutanen da ke kaunar kasar Sin suka kafa shi, da kawancen rukunonin dimokuradiya na kasar Sin, wanda masu ilmi da al'adu da kimiyya da fasaha bisa babba da matsakaicin matsayi suka kafa shi, da kungiyar kafa kasa ta dimokuradiya ta kasar Sin, wadda jama'ar da ke rukunin tattalin arziki suka kafa ta, da kungiyar sa kaimi ga aikin shimfida dimokuradiya ta kasar Sin, wadda masu ilmi da ke gudanar da aikin madaba'a bisa babba da matsakaicin matsayi suke ginshikinta, da Jam'iyyar dimokuradiya ta manoma da ma'aikatan masana'antu ta kasar Sin, wadda masu ilmin likitanci da magunguna bisa babba da matsakaicin matsayi suke ginshikinta, da Jam'iyyar Zhigong ta kasar Sin, wadda take kunshe da Sinawa da suka komo gida da iyalansu bisa babba da matsakaicin matsayi, da kungiyar al'umma ta Jiusan ta kasar Sin, wadda masu ilmi da fasaha bisa babba da matsakacin matsayi suke ginshikinta, da kuma kawancen tafiyar da harkokin kansu na dimokuradiya na Taiwan, wanda jama'ar lardin Taiwan na kasar Sin suka kafa shi.

Jam'iyyun dimokuradiya na kasar Sin sun zama babbar abokiya ta Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, wadanda suke aiwatar da harkokin siyasa da hadin kai da Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, kuma su ba jam'iyyun adawa ko jam'iyyun da ba su da ikon tafiyar da harkokin siyasa ba ne. Jam'iyyun dimokuradiya na kasar Sin sun zama mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, wadda ita ce kungiyar kawancen kaunar kasar Sin da dinkuwar kasar Sin da Jam'iyyar Kwaminis ta Sin take shugbanta. Jam'iyyun dimokuradiya na kasar Sin sun hada kansu da Jam'iyyar Kwaminis ta Sin bisa hanyar ba da shawarwari kan harkokin siyasa da sa ido irin na dimokuradiya, ta haka sun shiga cikin harkokin siyasa, da yin shawarwari kan manyan manufofin kasar Sin da zaben shugabannin kasar, da kula da harkokin kasar Sin, da gudanar da aikin tsara dokoki da shari'ar kasar Sin da kuma aiki da su.(Danladi)