Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 19:33:35    
Tambarin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da kuma tutarta

cri

A kan jan tambarin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, an yi zanen rawayun guduma da lauje, wadanda suke hade da juna. Launin ja yana almantar da juyin mulki, sa'an nan kuma, rawayun guduma da lauje alama ce ta kayan aiki da ma'aikata da manoma ke amfani da su. Dukkansu sun almantar da cewa, Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin kungiyar kan gaba ce ta ajin ma'aikata, tana almantar da babbar moriyar ajin ma'aikata da kuma fararen hula.

A kan jan tutar Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, an yi zanen tambari mai ruwan zinariya na jam'iyyar.

Tambarin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da kuma tutarta alama ce ta Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin. Ya zama wajibi hukumomin jam'iyyar na matakai daban daban da kuma ko wane dan jam'iyyar su kiyaye mutuncin tambarin jam'iyyar da tutar jam'iyyar, haka kuma, su kera da kuma yin amfani da su bisa ka'idojin da aka tsara.