Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 19:32:57    
Hukumomin sanya ido wajen ladabtarwa na JKS

cri

Hukumomin sanya ido wajen ladabtarwa na jam'iyyar kwaminis ta Sin hukumomi ne da ke sanya ido a kan yadda rassan jam'iyyar da kuma 'yan jam'iyyar ke bin dokokin jam'iyyar, tare kuma da hukunta wadanda suka karya dokokin. Hakkokin da hukumomin ke da su sun hada da: sanya ido da tuhuma da bincike da ba da shawara da yanke hukunci da kuma tsara dokokin jam'iyyar kwaminis ta Sin.

Hukumomin sanya ido wajen ladabtarwa na jam'iyyar kwaminis ta Sin sun hada da hukumar tsakiya ta sanya ido wajen ladabtarwa da hukumomin sanya ido wajen ladabtarwa na wurare daban daban da dai sauran kananan hukumomin sanya ido.

Babban nauyin da ke bisa wuyan hukumomin na matakai daban daban ya hada da kiyaye tsarin dokokin jam'iyyar kwaminis ta Sin da dai sauran ka'idojin jam'iyyar, da bincike kan yadda ake aiwatar da manufofin jam'iyyar da kuduranta, da kuma taimaka wa kwamitocin jam'iyyar wajen inganta da'a a cikin jam'iyyar da kuma daidaita ayyukan yaki da cin hanci da rashawa.

Hukumomin sanya ido wajen ladabtarwa na jam'iyyar kwaminis ta Sin su kan ladabtar da 'yan jam'iyyar a kai a kai, su kan kuma tsai da kudurai dangane da kiyaye dokokin jam'iyyar. Sa'an nan, suna sanya ido kan yadda shugabanni 'yan jam'iyyar ke tafiyar da iko, tare kuma da binciken al'amura masu tsanani na karya tsarin dokokin jam'iyyar da dai sauran ka'idojin jam'iyyar da rassan jam'iyyar da 'yan jam'iyyar suka yi da kuma yanke hukunci a kan 'yan jam'iyyar, ko kuma janye hukunci. Bayan haka, suna kuma kula da kararrakin da 'yan jam'iyyar suka kai musu da kuma tabbatar da hakkin 'yan jam'iyyar.(Lubabatu)