Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 19:32:26    
Babba taron wakilai na duk kasa na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin

cri

Bisa abubuwan da aka tanada cikin kundin Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, an ce, babban taron wakilai na duk kasa ta Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da kuma kwamitin tsakiya da ya fitar da shi, su zama hukumomin shugaba na koli na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, babban taron wakilai na duk kasa ya tattauna da yanke shawara kan manyan batutuwan jam'iyyar. Ayyuka da kuma iko na babban taron wakilai na duk kasa su ne, saurara da kuma bincike kan rahoton daga kwamitin tsakiya, saurara da kuma bincike kan rahoton daga kwamitin tsakiya mai kula da harkokin da'a, tattauna da yanke shawara kan manyan batutuwan Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, yi gyara kan kundin jam'iyyar, zabi kwamitin tsakiya, zabi kwamitin tsakiya mai kula da harkokin da'a na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin.

A kan shirya babban taron wakilai na duk kasa ta Jam'iyyar Kwaminis ta Sin a ko wane shekaru 5. A zabi wakilan da suka halarci babban taron duk kasa na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin daga hukumomin zabe na larduna da jihohi masu ikon tafiyar da harkokin kansu da biranen da gwamnatin tsakiya take shugabanta kai tsaye da sojojin 'yantar da jama'a na kasar Sin. Ana zabar ko wane wakili ne ta hanyar gabatar da shi da kuma zabe shi, sa'an nan kuma, 'yan Jam'iyyar Kwaminis ta Sin sun jefa kuri'a kan su ba tare da sanya suna ba kuma bisa tsarin 'yan takara sun fi guraben takara yawa. Domin tabbatar da cewa, wadannan wakilai sun waklici ra'ayi da kuma burin 'yan Jam'iyya da jama'ar kasar Sin, hukumomin zabe su kan yi rangadi kan wadannan wakilai, wato su kan saurari ra'ayin jama'a, jama'a su iya sa ido kan wadannan wakilai.

A watan Yuli na shekarar 1921 a birnin Shanghai, Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta shirya babban taron wakilai na duk kasa na karo na farko. Babban taron ya zartas da tsarin ka'ida na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, inda aka bayyana babban makasudin Jam'iyyar a fili. Ban da wannan kuma, babban taron ya tattauna kan halin da ake ciki a lokacin, da kuma babban aikin Jam'iyyar, da ka'idoji da hukumomin Jam'iyyar da dai sauran batutuwa. Kirar babban taron wakilai na duk kasa na karo na farko ya sanar da kafuwar Jam'iyyar Kwaminis ta Sin.(Danladi)