Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 18:05:11    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin.

cri

---- Jami'in hadaddiyar kungiyar nakasassu ta kasar Sin ya bayyana cewa, cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, sha'anin nakasassun kasar Sin ya samu ci gaba da saurin gaske, gwamnatocin matakai daban-daban sun yi kokarin taimakawa nakasassau, tun ba nakasassu 'yan kananan kabilu ba wajen samun aikin yi.

A gun gasar nuna fasahar sana'o'i ta karo na 3 ta nakasassun duk kasa, Mr. Wang Xinxian, mataimakin shugaban hadaddiyar kungiyar nakasassu ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin tana da nakasassau fiye da miliyan 80, daga cikinsu da akwai jahilai da ba wadanda jahilai sosai ba wadanda yawansu ya kai fiye da miliyan 30, musamman ma nakasassun da ke shiyyoyin kananan kabilu ba su samu damar koyon fasahar sana'o'i ba sakamakon rashin ci gaban tattalin arziki da sauran matsalolin da ake gamuwa da su a wadannan wurare. Sabo da haka, gwamnatoci na matakai daban-daban na kasar Sin sun yi ayyuka da yawa wajen samar wa nakasassu aikin yi.

---- Bisa labarin da aka bayar a ran 30 ga watan Agusta daga birnin Lhasa na jihar Tibet ta kasar Sin an ce, yanzu lokaci ya yi domin yin yawon shakatawa a jihar Tibet, masu yawon shakatawa da yawa da suka zo daga kasashen waje suna yin yawo a wannan wurin da ake kira kololuwan duniya, amma ba su gamuwa da wahalhalu wajen harshe ba lokacin suke yawon shakatawa, ko sayen kayayyaki da sauran harkokin zaman yau da kullum.

A kan shahararen titin Barkor da ke kewayen dakin ibada mai suna Jokhan na birnin Lhasa, ana iya jin sautin karatun da mabiyan addinain Buddaha na Tibet suka yi, kuma nan ne cibiyar yin yawon shakatawa da ciniki mafi wadata ta birnin Lhasa, kullum ana iya ganin masu yawon shakatawa masu launin fata daban-daban wadanda suka zo daga kasashen waje suna ta kai da kawowa a kan wannan titi.

---- Mun sami labari a ran 29 ga watan Agusta cewa, jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin ta yi kokarin bunkasa tashoshin kwastan da ke bakin iyakar kasa tsakanin Sin da Rasha, wannan ya sa kaimi sosai ga bunkasa cinikayyar da ake yi tsakanin kasar Sin da Rasha.

Mr. Meng Guixi, mataimakin shugaban hukumar kasuwanci ta jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta ya bayyana cewa, yanzu jihar tana da tashoshin kwastan 5 da ke bakin iyakar kasa tsakanin Sin da Rasha. Wadannan tashoshin kwastan suna da halayen musamman wajen gudanar da harkokinsu da sauri kuma cikin tsimi, kuma sun sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin jihar Mongoliya ta gida tare da kasashen waje.