Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-14 20:06:32    
Yawan jarin da Sin ta zuba kai tsaye a kasashen waje a shekarar 2006 ya wuce dalar Amurka biliyan 20

cri
A yau ranar 14 ga wata a nan birnin Beijing, ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin da dai sauran sassa daban daban sun bayar da wata sanarwa dangane da jarin da Sin ta zuba wa kasashen waje kai tsaye a shekarar 2006. Sanarwar ta yi nuni da cewa, a shekarar bara, yawan kudaden jarin da Sin ta zuba wa kasashen waje kai tsaye ya kai dalar Amurka fiye da biliyan 21, wanda ya zo na 13 a duk duniya. A cewar wani jami'in ma'aikatar kasuwanci ta Sin, bisa bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, Sin za ta kara saurin zuba jari kai tsaye a kasashen waje.

Mr.Chen Lin, mataimakin shugaban sashen kula da harkokin hadin kan tattalin arziki da kasashen waje na ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya bayyana cewa, daga shekarar 2002 zuwa 2006, matsakaicin saurin karuwar jari da Sin ta zuba wa kasashen waje kai tsaye a fannin kadarori ya kai har kashi 60%. Ya ce,"A cikin 'yan shekarun nan, bisa bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, ya zama dole a zuba jari a kasashen waje. A ganinmu, bisa bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a nan gaba, musamman ma a yayin da aka shiga wani sabon mataki wajen shigowa da jarin waje, tabbas ne za mu kara saurin zuba jari a kasashen waje."

A sa'i daya, Mr.Chen Lin ya kuma bayyana cewa, ko da yake a cikin 'yan shekarun baya, jarin da Sin ta zuba a kasashen waje ya karu da sauri, amma duk da haka, jarin kadan ne idan an kwatanta shi da na duniya baki daya. Bisa sanarwar, kawo karshen shekarar 2006, gaba daya yawan kudaden jarin da Sin ta zuba a waje ya kai dalar Amurka kimanin biliyan 90 ne kawai, wanda bai kai kashi daya daga cikin 20 na Amurka ba.

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, kamfanonin Sin kusan dubu 10 da ke zuba jari a kasashen waje suna barbazuwa a kasashe da shiyyoyi 172 na duk duniya, kuma ma'aikatan da kamfanonin suka dauka daga kasashen ya kai dubu 290. Kamfanonin sun samar da dimbin guraben aiki ga kasashen, sun kuma sami karbuwa daga wajensu. A cewar Mr.Chen Lin, matakimakin shugaban sashen kula da harkokin hadin kan tattalin arziki da kasashen waje na ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin, ko da yake Sin ba ta fara zuba jari a kasashen waje tun da wuri ba, kuma ya kasance da gibi a tsakaninta da kasashe masu sukuni a wannan fanni, amma Sin za ta kara ba da jagoranci a kan kamfanoninta, ya ce,"za mu kayyade ayyukan zuba jari da kamfanoninmu suke yi a kasashen waje, ciki har da nuna biyayya ga dokokin kasashen da kuma nuna kulawa ga moriyar jama'arsu. Sabo da haka, muna ganin zuba jari da muke yi a kasashen waje ya dace da bunkasuwar tattalin arziki, haka kuma ya dace da moriyar al'umma da ta jama'a na kasashen."

An ce, sanarwar da aka bayar a yau dangane da jarin da Sin ta zuba kai tsaye a kasashen waje, ta sami wasu gyare-gyare ta fuskar hanyoyin da aka bi wajen yin kididdigar. Mr.Wang Kechen, mataimakin shugaban sashen kula da kirgar cinikin waje na hukumar kula da kididdiga ta kasar Sin, ya ce, adadin kididdigar ya dace da hanyoyin da kasa da kasa ke bi wajen yin kididdiga, ya ce,"wannan ya kasance kididdigar da ya dace da hanyoyin da kasa da kasa ke bi wajen yin kididdiga. Bisa kundin bayani na biyar kan samun daidaito a harkokin ciniki na asusun ba da lamuni na duniya, mun yi gyare-gyare a kan tsarinmu sannu a hankali, yanzu tsarinmu ya riga ya cancance shi daga dukan fannoni."(Lubabatu)