Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-12 17:56:16    
Ana soma daukar sinimar hukuma dangane da wasannin Olimpic na birnin Beijing

cri

A watan Augusta na shekara mai zuwa, za a yi wasannin Olimpic da kowa ya zura ido a kai a nan birnin Beijing na kasar Sin, kwanan nan, ana soma daukar sinimar hukuma dangane da wasannin Olimpic, kuma a watan Maris na shekara mai zuwa , za a soma daukar sinima bisa babban mataki.

A wasannin Olimpic da aka shirya a Stockolm a shekarar 1912, an samu sinimar farko ta hukumar wasannin Olimpic. Daga nan, daukar sinimar hukuma ya zama aiki mai muhimmanci da abin alfahari mai girma sosai ga kwamitin shirya wasannin Olimpic na farko. Babbar dawainiyar sinimar hukuma ita ce don daukar hakikanan abubuwan da aka yi a gun wasannin Olimpic da aka yi a wannan gami daga dukan fannoni da kuma bayyana gasannin motsa jiki da ke burge mutane sosai da sosai da kuma labaran da suka faru bayan gasannin, sinimar ta kunshe da tanada abubuwan tarihi masu daraja sosai da yawa, ya zuwa yanzu, mutane masu kishin zaman lafiya da motsa jiki na duk duniya suna burge sosai da sosai bisa sakamakon daukar sinimar.

A gun wasannin Olimpic da za a shirya a birnin Beijing a shekarar 2008, za a kuma dauki wata sinimar hukuma da ke da lakabi haka: "Wasannin Olimpic na birnin Beijing" wadda za ta zama ta 22 a tarihin wasanni Olimpic. Yanzu, kungiyar daukar sinimar ta riga ta kafu, mai ba da jagorancin daukar sinima na ma'aikatar daukar sinimar watsa labaru ta tsakiya ta kasar Sin mai suna Gu Yun ta zama mai jagorar sinimar, ta bayyana cewa, daukar sinimar hukuma dangane da wasannin Olimpic, da farko, ya wakilci kwamitin wasannin Olimpic na kasashen duniya, na biyu, ya wakilci kwamitin wasannin Olimpic na birnin da ya shirya wasannin Olimpic, sa'anan kuma ya wakilci birnin da ya shirya wasannin Olimpic, a karshe dai ya wakilci wadanda suke da hannun daukar sinimar da kungiyar da ta hada da masu ba da jagorancin sinimar, wannan ne babban bambancin da ke tsakaninta da sauran sinimar da aka dauka, sinimar ta yi magana a madadin hukuma.

Bisa shirin da aka tsai da, an bayyana cewa, a watan Maris na shekara mai zuwa, kungiyar daukar sinima dangane da wasannin Olimpic da za a shirya a birnin Beijing za ta zafi manyan nahiyoyin duniya 5 don daukar sinima dangane da rukunoni biyar na 'yan wasannin motsa jiki don bayyana yadda 'yan motsa jiki na kasashe daban daban da shiyyoyi daban daban na duniya suka shirya da halarci wasannin motsa jiki , an bayyana cewa, za a yi shirin daukar sinimar bisa fatansu na samun jituwa a duniya. Mai daukar sinimar Wu Qi ya bayyana cewa, jituwa ba wani ra'ayi maras amfani ba, jituwa tana hada abubuwa iri iri masu bambanci sosai kuma tana iya hakuri da abubuwa masu bambanci da yawa, saboda haka wasannin Olimpic ya samar da wani sarari, wato wasannin Olimpic ya zama wani abun da yake iya hakuri da abubuwa da yawa, watakila 'yan wasan motsa jiki za su iya yaki da juna bayan da suka koma gida, amma, a wurin gasar da aka shirya, su ne suke zama cikin jituwa. Ba za mu iya tsirar da mu wajen daukar sinima dangane da rikicin siyasa da rikicin al'adu da ke kasancewa a tsakaninsu ba, akasin haka, za mu daukar sinimar da za ta iya bayyana irin rikici, kodayake a Gabas ta tsakiya da akwai hadari gare mu, amma ya kamata mu tafi wata shiyyar da ke gabas ta tsakiya don daukar wasu abubuwa a cikin sinimar, sa'anan za mu hada wadannan abubuwa da gasannin da za a yi a wasannin Olimpic na Beijing gu daya don bayyana dawainiya da al'adu da 'yan adam suke fuskanta. Yadda za a dauki sinimar a wurin da zai shirya wasannin Olimpic , Mr Wu Qi ya bayyana cewa, yawan 'yan wasan motsa jiki na kasar Sin da za a dauke su ba zai iya wuce na sauran kasashe ba.

Za a bayyana babban batun sinimar da ke cewar " Duniya daya kuma mafarki daya" ta hanyar wani gini ko wani iyali ko wata hanyar gudu ko 'yan wasa na wata kungiya ko wani rukunin 'yan sanda da dai sauransu.(Halima)