Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-12 08:55:13    
Liu Xiang ya sake samun babbar nasara a tarihin wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasar Sin

cri
Ran 2 ga wata, a birnin Osaka na kasar Japan, an rufe gasar fid da gwani ta wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasa da kasa a karo na 11. A cikin gasar karon karshe na wasan gudu tare da ketare shinge mai tsawon mita 110 da aka yi a tsakanin maza a ran 31 ga watan Agusta, dan wasa Liu Xiang na kasar Sin ya zama zakara bayan da ya sami lambar zinariya a gun taron wasannin Olympic da kuma samar da sabon matsayin bajimta na duniya, ya sake yin abin tarihi a tarihin wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasar Sin.

Lambar zinariya da Liu Xiang ya samu, ta zama ta farko ce da 'yan wasan Sin maza suka samu a tarihin gasar fid da gwani ta wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya da aka yi har sau 11, haka kuma, lambar zinariya daya kacal da kasar Sin ta samu, har ma dukkan 'yan wasan kasashen Asiya suka samu a gun gasar fid da gwani ta duniya a wannan shekara. A sa'i daya kuma, ta kasance ta farko da 'yan wasan Sin suka sake samu a gun gasar fid da gwani ta duniya bayan shekaru 8. Bayan gasar, Liu Xiang ya yi zumudi sosai, ya ce,'Babu tantama na yi zumudi kwarai. Saboda ban yi fintikau yadda ya kamata a wannan karo ba, irin wannan gasa ta matsayin duniya ta ba ni matsala a tunanina. Ban saki jiki yadda ya kamata ba a cikin gasar, shi ya sa, na fi saura sauri kadan kawai. Na yi matukar zumudi. Na sami nasara, na zama zakara a gun gasar fid da gwani ta duniya. Yana da kyau ainun.'

Wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasar Sin ya shiga zamani mafi ci gaba a shekarun 1990. Amma a cikin sabon karnin da muke ciki, saboda shahararrun 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasar Sin sun yi ritaya, haka kuma, kasar Sin ta rasa samun isassun 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle matasa, shi ya sa ta koma baya sosai. Kafin gasar fid da gwani ta duniya da aka yi a Osaka, 'yan wasan Sin ba su sami lambar zinariya a gun gasar fid da gwani ta duniya ba har karo 3 a jere. Bullowar Liu Xiang ta kawo sauye-sauye ga halin da kasar Sin ke ciki a wasan guje-guje da tsalle-tsalle, wato a da makin da 'yan wasa mata suka samu ya fi na maza kyau, sa'an nan kuma, ta ba mutane kyakkyawan fata na ganin 'yan wasan Sin za su zama zakara a gun taron wasannin Olympic da gasar fid da gwani ta duniya.

A matsayin sabon jagora a tsakanin 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasar Sin, Liu Xiang ya zama zakara a cikin gasar gudu tare da ketare shinge mai tsawon mita 110 a gun taron wasannin Olympic na Athens na shekarar 2004, ya zama dan Asiya na farko da ya zama zakara a cikin gasannin gudu na gajeren zango a gun taron wasannin Olympic. A shekarar 2006, ya karya matsayin bajimta na duniya na wasan gudu tare da ketare shinge mai tsawon mita 110, wanda ba a karya shi ba har shekaru 13. A gun gasar fid da gwani ta duniya da aka yi a Osaka, karo na 4 ne da Liu Xiang ya shiga wannan muhimmiyar gasa, a karshe dai, ya cimma burinsa na zama zakara a gun gasar fid da gwani ta duniya. Ya ce,'Na kyautata makina a ko wane karo, na sami ci gaba a mataki mataki. Ina neman samun ci gaba sannu a hankali bisa matakan da na tsara.'

Ko da yake Liu Xiang ya zama zakara a gun taron wasannin Olympic da gasar fid da gwani ta kasa da kasa, yana kuma rike da matsayin bajimta na duniya, amma bayan gasar, ba tare da boye abubuwa ba ya nuna cewa, zama zakara a Osaka bai sassauta matsin lambar da yake fuskanta sosai ba, domin an dauka masa nauyin zama zakara a gun taron wasannin Olympic na Beijing a shekara mai zuwa.

Game da taron wasannin Olympic na shekara mai zuwa, malam Sun Haiping, malamin horas da wasanni da ke horar da Liu Xiang, ya bayyana cewa, yana kasancewa da babbar matsin lambar zama zakara, amma zai yi ayyuka ta hanyar kimiyya yadda ya kamata domin tabbatar da 'yan wasan Sin maza su ci gaba da zama kan gaba a cikin gasar gudu tare da ketare shinge mai tsawon mita 110. Ya ce,'Taron wasannin Olympic na shekara mai zuwa makasudin karshe ne a gare mu. Ba za mu iya tabbatar da makasudinmu ba, sai mu sami lambar zinariya a shekara mai zuwa. Shi ya sa ko da yake mun sami lambar zinariya a gun gasar fid da gwani ta duniya a shekarar bana, amma ya zuwa yanzu muna fuskantar matsin lamba, domin za a yi taron wasannin Olympic a Beijing a shekara mai zuwa, a mahaifiyarmu. Tabbas ne za mu fuskanci babbar matsin lamba, in an kwatanta ta da wadda muke daidaita a Osaka. A zahiri kuma, tun daga yanzu mun tsara takaimaiman shirye-shirye na share fage ga taron wasannin Olympic.'

Yanzu zama zakara a gun gasar fid da gwani ta duniya ya zama tarihi, ko Liu Xiang zai sake samun babbar nasara a gun taron wasannin Olympic na Beijing a shekara mai zuwa ko a'a ya janyo hankulan mutane.(Tasallah)