Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-12 08:53:21    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(06/09-12/09)

cri
Ran 6 ga wata rana ce ta murnar sauran shekara daya da bude taron wasannin Olympic na nakasassu na Beijing. Shugaba Liu Qi na kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing da shugaba Philip Craven na kwamitin wasan Olympic na nakasassu na kasa da kasa sun aika da takardun gayyata ga kwamitocin wasan Olympic na nakasassu na kasa da kasa da na yankuna daban daban na duniya a ran nan, inda cikin sahihanci ne suka gayyace su da su shiga taron wasannin Olympic na nakasassu da za a yi a nan Beijing a shekara mai zuwa. Ban da wannan kuma, a wannan rana da dare, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya kaddamar da kasafin hanyar da za a bi wajen bai wa juna wutar yola ta taron wasannin Olympic na nakasassu na Beijing. Za a yi taron wasannin Olympic na nakasassu a Beijing tun daga ran 6 zuwa ran 17 ga watan Satumba na shekara mai zuwa.

Wata sabuwa kuma, a ran 4 ga wata, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya sanar da cewa, tun daga ran 5 ga wata na shekarar da muke ciki zuwa ran 30 ga watan Afril na shekara mai zuwa, zai tattara hotonan murmushin yara daga duk duniya. Mai yiwuwa ne zai yi amfani da wadannan hotona a cikin wasannin kwaikwayo na bukukuwan bude da rufe taron wasannin Olympic na Beijing.

Ran 10 ga wata da dare, a birnin Shanghai na kasar Sin, an bude gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta mata da hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasa da kasa wato FIFA ta shirya a shekarar 2007. Madam Chen Zhili, wakiliyar majalisar gudanarwa ta kasar Sin kuma shugabamai daraja ta kwamitin shirya gasar cin kofin duniya a wannan karo da kuma shugaba Sepp Blatter na kungiyar FIFA sun halarci bikin bude gasar. Kungiyoyin kasashe 16 suna takara da juna don zama zakara a biranen Tianjin da Shanghai da Hangzhou da Wuhan da kuma Chengdu tun daga ran 10 zuwa ran 30 ga wata.

Ran 8 ga wata, a cibiyar wasan kwallon tennis ta Beijing, an bude budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta kasar Sin ta shekara ta 2007. 'Yan wasa fiye da 300 da suka hada da Nikolay Davydenko da Fernando Gonzalez da Justine Henin da Martina Hingis da sauran kwararru sun shiga gasar. Za a rufe wannan gasa a ran 23 ga wata.

Ran 9 ga wata, a cikin gasar ba da babbar kyauta ta wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasa da kasa da hadaddiyar kungiyar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasa da kasa ta shirya a kasar Italiya, shahararren dan wasa Colin Powell na kasar Jamaica ya karya matsayin bajimta na duniya na gudun mita 100 da ya rike da shi, sabon matsayin bajimta na duniya shi ne dakikoki 9.74.(Tasallah)