Ko kuna tsammanin cewa, abin da kuka saurara dazun nan wasannin fasaha ne da Sinawa suka nuna? A'a, a hakika dai ba haka ba ne. Kasashen waje gaba da daya ne suka nuna wannan. Kuma daliban kasashen waje ne da suka shiga zagaye na karshe na gasa ta shida ta yin magana da Sinanci wadda ake kiranta "gadar Sinanci".
'Yan wasa na kasashen waje fiye da dari da suka zo daga kasashe 52 sun shiga karon karshe na gasar "gadar Sinanci" da aka yi a birnin Changchun da ke arewa maso gabashin kasar Sin a farkon watan Agusta na shekarar da muke ciki. Dukkansu suna iya Sinanci sosai, kuma suna fahimtar tarihi da al'adun gargajiya da wuraren yawon shakatawa na kasar Sin, ban da kuma suna iya nuna wakoki da rubutu da kayayyakin kida da zane-zane da kuma Kongfu na kasar Sin kamar yadda ya kamata. To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan kaunar da baki masu koyon harshen Sinanci suka nuna wa kasar Sin.
A cikin 'yan wasa da suka shiga karon karshe na gasar, wani saurayi mai suna Theppahaphone Bounyavong da ya zo daga kasar Laos ya yi farin jini sosai. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da ba kawai yana iya magana da Sinanci kamar yadda ya kamata ba, har ma yana da wani sunan Sinanci irin daya tare da wani shahararren tauraro na kasar Sin wato Liu Dehua. Kuma ya gaya wa wakilinmu cewa,
"Mahaifiyata ta ba ni wannan sunan Sinanci na Liu Dehua, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da ta nuna sha'awa sosai ga wakokin da Mr. Liu ya rera da kuma wasannin kwaikwayon da ya sa hannu a ciki. Sabo da haka kuma ta kai ni zuwa makaranta domin koyon Sinanci."
Sannu a hankali, Theppahaphone Bounyavong ya gano cewa, Sinanci da kuma al'adun gargajiya na kasar Sin sun riga sun zama jiki gare shi, shi ya sa lokacin da yake neman shiga jami'a, ya zabi ilmin Sinanci ba wata-wata. A idonsa, sarrafa Sinanci yana da amfani sosai. Kuma ya bayyana cewa,
"Na gano cewa, ana iya samun Sinawa a ko wace kasa ciki har da kasar Laos. Idan na iya Sinanci sosai, to bayan da na gama karatu daga jami'a, zan iya yin cinikayya tare da Sinawa, ko kuma zama wani mai fassara. Ta haka zan iya samu kudade da yawa."
A hakika dai, yanzu yawan baki da suke koyon harshen Sinanci ya riga ya zarce miliyan 30, daga cikinsu, 'yan kasashen Laos da Vietnam da Thailand da Korea ta Kudu da kuma Japan da ke kusa da kasar Sin sun fi yawa, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da al'adun kasashen nan ya yi kusa da na kasar Sin, a waje daya kuma sun yi cudanya sosai tare da Sin, sabo da haka koyon Sinanci ya yi farin jini sosai a kasashen.
Ban da wannan kuma, tare da kara bude kofa ga kasashen waje da kasar Sin ke yi da kuma karuwar saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar, yanzu Sin tana kara yin cudanya da tuntuba tare da duniya. Bisa matsayinsa na wata muhimmiyar hanya wajen fahimtar kasar Sin, Sinanci ya samu karbuwa sosai daga wajen mutanen kasashen Turai da Amurka har ma na Afirka.
Jonathan Kent wanda ke son nazarin al'adun gargajiya na kasar Sin wani dalibi ne na jami'ar princeton ta kasar Amurka. Kuma wannan shi ne karo na farko da ya shiga gasar "gadar Sinanci" ta managa da Sinanci. Lokacin da yake tabo kaunar da yake nuna wa Sinanci, ya bayyana cewa, ya riga ya koyi Sinanci har shekaru 3, kuma ya shirya wani shirin sarrafa harshe da ke iya nuna al'adun gargajiya na kasar Sin sosai domin gasar.
Kuma Jonathan Kent ya yi bayani cike da alfahari, cewa dimbin Sinawa ba su taba karanta muhimman littattafan tarihin kasar Sin ba, kamar Lunyu da Mengzi da Zhuangzi da kuma Shiji, amma ya karanta dukkansu. Yanzu yana nuna sha'awa sosai ga kagaggun labarai na Kongfu na kasar Sin. Kuma ya kara da cewa,
"yanzu ina karanta wani shahararren kagaggen labari na kasar Sin wanda ake kiransa 'labarin Luding', kuma shi ne littafin adabin kasar Sin da na fi so. "
Jonathan Kent na kasar Amurka da kuma Thepphaphone Bounyavong na kasar Laos wata shaida ce ta baki fiye da miliyan 30 masu koyon Sinanci da sha'awar Sinanci. Yanzu kasar Sin tana nuna halinta na musamman a gaban duk duniya bisa bunkasuwar tattalina arziki cikin sauri da kuma al'adun gargajiya mai zurfi, ta haka ya jawo hankulan dubban 'yan kasashen waje wajen fahimtar kasar Sin ta hanyar koyong Sinanci.(Kande Gao)
|