Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-11 18:51:41    
Sin tana son tinkarar sauyin yanayi tare da kasashe daban daban

cri

Mataimakin firaministan kasar Sin, Zeng Peiyan ya bayyana a ranar 11 ga wata cewa, Sin tana son hada kanta da kasashen duniya, domin tinkarar sauye-sauyen yanayin duniya.

a ran nan a nan birnin Beijing, an bude taron dandalin tattaunawa a tsakanin wadanda suka samu lambobin yabo na Nobel na shekarar 2007. A gun bikin bude taron, Mr.Zeng Peiyan ya bayyana cewa, taron dandalin zai samar da wani dandali mai kyau ga masu ilmin kimiyya da gwamnatoci na kasashe daban daban wajen aiwatar da hadin gwiwa.

Mr.Zeng Peiyan ya ce, game da matsalar karuwar albarkatun kasa da ake amfani da su a lokacin da ake samun karuwar tattalin arziki tare kuma da matsalar sauye-sauyen yanayi, Sin za ta tsaya tsayin daka kan manufar samun dauwamammen cigaba, za ta dora muhimmanci kan yin kirkire-kirkire bisa karfin kanta da kuma rage amfani da makamashi da rage fitar da sinadarai masu guba. Ban da wannan, Sin za ta kuma yi kokarin bunkasa na'urorin nukiliya na samar da wutar lantarki, za ta kara yin amfani da makamashin ruwa da na iska da na rana wadanda ke iya sabuntawa.(Lubabatu)