Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-10 20:58:46    
A kara fahimtar juna da samu ra'ayi daya da ciyar da hakin kai gaba

cri

A cikin shirinmu na yau za mu karanta wani bayanin da wakilin gidan rediyonmu ya ruwaito mana.Tun daga ran 3 zuwa ran 9 ga watan Satumba,shugaban kasar Sin Hu Jintao ya kai ziyarar aiki a kasar Australiya kuma ya halarci kwarya kwaryar taron shugabani a karo na 15 na kungiyar APEC da aka yi a Sydney.Ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya bayyana cewa wannan ziyarar da shugaban kasa Hu Jintao ya yi wani muhimmin aikin diplomasiya ne a gabannin kiran taron wakilan kasa na 17 na Jm'iyyar Kwaminis ta Sin,yana da muhimmiyar ma'ana ga bunkasa dangantaka da ke tsakanin kasar Sin da Australiya haka kuma ga hadin kan bangaren Ashiya da na Pacific.

A cikin jirgin saman kasar Sin dake kan hanyar komawa gida daga Australiya,Ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya yi hira da maneman labaran da suka rufa wa shugaban kasa gun ziyara,inda ya tattara sakamakon da aka samu daga wannan ziyara ta shugaban kasa Hu Jintao.Ya ce "Wannan ziyarar da shugaban kasa Hu Jintao ya y,wani muhimmin aikin diplomasiya ne na kasar Sin a wannan shekara a bangaren Asiya da na Pacific.Shugaba Hu Jintao ya yi ayyuka da dama ciki har da halartar tarurruka na bangarori biyu da na bangarori da dama sama da 40.Ziyararsa ta samu sakamako.Na farko shi ne ya yi mu'amala da bangarori,da ciyar dangantakar dake tsakanin Sin da Australiya gaba."

Shiga kwarya kwarya taron shugabanni na kungiyar APEC,wani muhimmin aiki ne dabam a cikin ziyarar Hu Jintao.Mr Yang Jiechi ya ci gaba da cewa "Sakamako na biyu da aka samu a cikin wannan ziyara shi ne shugaban kasa ya bayyana manufofin da kasar Sin ta dauka,ya kuma sa kaimi ga cigaban hadin kan Asiya da Pacific."

A lokacin da yake halartar taron,shugaban kasar Sin Hu Jintao ya bayyana manufofin da gwamnatin kasar Sin ta dauka kan muhimman batutuwan da suka shafi moriyar bangarori da na duniya baki daya,ya kuma bayyana matsayin da kasar Sin ta tsaya a kai na daukar nauyi da yin hadin kai mai amfani da ciyar da hadin kan Asiya da Pacific gaba lami lafiya.Matsalar sauye sauyen yanayi,wani muhimmin batu ne da ya fi daukar hankali a taron.A kan matsayin kasa mafi girma daga cikin kasashen matasa,matsayin da kasar Sin ta dauka da shawarwarin da ta kawo sun fi jawo hankulan mutane.A gun taron,shugaba Hu Jintao ya kawo shawarwari guda hudu wato nacewa ga hadin kai wajen tinkarar canzawar yanayi,da nace ga neman samun dauwamammen cigaba,da nacewa ga mai da "yarjejeniyar sauye sauyen yanayi na MDD" a matsayin jagora,da nacewa ga bin hanyar kimiyya da fasaha,ya kuma gabatar da shawarar "yanar gizo ta internet wajen maido dazuzzuka a Asiya da Pacific da kula da su."Wannan karo ne na farko da gwamnatin kasar Sin ta gabatar da shawarar hakikani mai amfani kan hadin kai domin tinkarar sauye sauyen yanayi a gun taron kasa da kasa,shawarar nan ta samu yabo da goyon baya daga bangarori daban daban."Sanarwar Sydney" da aka zartas a gun taron ta nanata da cewa a nace ga bin ka'idar "daukar nauyi tare wanda ke da banbanci." Sanarwar ta hada shawarar da kasar Sin ta kawo kan shimfida yanar gizo ta internet game da maido dazuzzukan Asiya da Pacifici da kula da su.

Kan gudanar da hadin kan Asiya da Pacific,Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya bayyana cewa Kasar Sin ta tsaya a kan a nuna kwazo da himma wajen sai kaimi ga ci gaban shawarwarin Doha da samun sakamako,a gaggauta harhada manufofin tattalin arziki na bangarori ta hanyoyi daban daban.Ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya ci gaba da cewa "sakamako na uku da aka samu a cikin wannan ziyara,shugaba ya bayyana manufofin Sin na game da gida da waje,ta haka aka kara fahimtar juna da samun amincewa daga sauran kasashen duniya."

Kasashen duniya sun sa lura sosai kan ci gabana tattalin arzikin kasar Sin a halin yanzu da kuma tasirin da ta kawo wa duniya.Shugaban kasa Hu Jintao ya bayyana cewa kasar Sin za ta cigaba da canza salon da take bi wajen yin cinikayya da kasashen waje,za ta shigo da karin kayayyaki daga ketare,da sanya kokarin wajen kare hakkin mallakar ilimi,ta kuma yi kokarin daidaita ciniki na shigi da fici.Shugaban kasa Hu Jintao ya jaddada da cewa Gwamnatin kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan ingancin kayayyaki da tabbatar da shi,ta kuma dauki wasu muhimman matakai,tana so ta hada kanta da sauran bangarori domin karfafa ingancin kayayyaki a ciniki tsakanin kasa da kasa.Jawaban shugaba Hu Jintao ya jawo hankulan bangarorin da ya shafa,kafofin yada labarai na kasa da kasa sun bayar da labarai a kan wannan batu.

Ministan harkokin waje na Sin Mr Yang Jiechi ya ci gabaa da cewa "sakamako na hudu da aka samu wannan ziyara,shi ne shugaban kasar Sin ya yi ganawa da shugabanni na sauran kasashe,ta haka aka karfafa dangantakar amincin dake tsakanin Sin da sauran kasashen duniya. A lokacin da ya bakunci taron,shugaban kasa Hu Jintao ya gana da shugabanni na kasashe tara na Asiya da Pacific,ya samu ra'ayi daya da takwarorinsa na sauran kasashe kan batutuwa dangane da karfafa dangantakar aminci da hadin kai tsakanin bangarori biyu,da kara taimakon juna da hada kai kan batutuwa na duniya da na bangarori.Shugaba Hu Jintao ya yi musanyar ra'ayi da shugabanni na wasu kasashe kan cinikin duniya,sauye sauyen yanayi,da batun nukiliya na Korea ta arewa,da matsalar nukiliya ta Iran da matsalar Darfur ta kasar Sudan,inda ya gabatar da shawarar yin kokari tare da a gaggauta a daidaita matsalolin da abin ya shafa yadda ya kamata.(Ali)