Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-10 21:18:41    
Babban manajan kamfanin mai na kasar Sin ya yi watsi da sambatun banza na wai kasar Sin tana habaka yunkurin samun makamashi a ketare

cri

A gun kwarya-kwaryar taron koli na kungiyar hadin kan tattalin arziki na Asiya da tekun Pacific wato Apec da kuma sauran jerin tarurrukan da aka gudanar daga ran 2 zuwa ran 9 ga watan da muke ciki a birnin Sydney na kasar Austaliya, sauyin yanayi da samar da ingantaccen makamashi sun zama daya daga cikin muhimman batutuwan da aka tatttauna a kai. Mr. Fu Chengyu, babban manajan babban kamfanin haka mai kan tekuna na kasar Sin dake halartar taron ya yi jawabin cewa, lallai ya kasance da gurguntawar fahimta a cikin wasu da'i'rorin ketare a game da ayyukan gudanar da harkokin kasuwanci da kamfanonin makamashin kasar Sin suke yi a kasashen waje. Hakan ya fito da ra'ayin banza na cewar wai kasar Sin tana habaka yunkurin samun makamashi a ketare.

A gun wani taron musamman na kara wa juna sani kan ' batutuwan makamashi da sauyin yanayi da kuma na bunkasuwar yankunan Asiya da na tekun Pacific', Mr. Fu Chengyu ya furta cewa: " Samar da ingantaccen makamashi, da sauyin yanayi da kuma bunkasuwar tattalin arziki ba wai kalubale ne dake gaban wata kasa daya tilo ba. A zahiri dai, kalubale ne dake gaban dukkan 'yan adam. Babu wata kasa ko wani kamfani dake iya warware wadannan matsaloli. Saboda haka ne ake bukatar samun hadin gwiwa tsakanin gwamnatoci da kamfanoni da kuma masana'antu".

A wani fanni daban kuma,  sanin kowa ne, kamfanoni da masana'antu ciki har da na mai da iskar gaz sukan samo abubuwa mafi araha ta hanyar hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa.

Babban kamfanin haka mai kan tekuna na kasar Sin na daya daga cikin manyan kamfanonin man fetur na kasar Sin.A 'yan shekarun baya, kamfanin ya nuna himma da kwazo wajen tafiyar da harkokinsu kamar yadda ya kamata a kasashe sama da goma na ketare. Yanzu dai, kasar Sin na bukatar samun karin makamashi yayin da take samun bunkasuwar tattalin arziki. Bisa wannan hali dai, wasu mutane sun yi zaton cewa wai kasar Sin tana bidar makamashi da kuma sauran albarkatai a fadin duk duniya, har sun fito da ra'ayin cewa kasar Sin tana habaka yunkurin samun makamashi a ketare. Game da wannan batu, Mr. Fu Chengyu ya fadi cewa: " Hadiye kamfanoni da masana'antu, bukata ce ta bunkasuwar wani kamfani. Ba wai kasar Sin ita ce kawai take bukatar makamashi ba. Sauran kamfanoni da masana'antu na duniya su ma haka suke yi har ma sun fi mu tafiyar da irin wadannan harkokin kasuwanci. ''

Kazalika, Mr. Fu Chengyu ya yi nuni da cewa, dukkan kamfanoni da masana'antu ciki har da na mai na kasar Sin sukan fi mai da hankali kan yadda za su kara yin amfani da makamashinsu na kansu. Yanzu kasar Sin tana rike da matsayin samun bunkasuwar tattalin arziki kamar yadda ya kamata; A lokaci daya kuma tana kokarin yin amfani da fasahohin zamani don rage yawan makamashin da take amfani da shi. Mr. Fu ya furta cewa: " Idan an yi la'akari ta fuskar kasuwanci, to ba dole ne kamfanonin makamashi su je can nesa ba kusa ba domin hakar mai domin makudan kudade ne sukan kashe. Ana ganin cewa, babu wani kamfani ko masana'antu dake kashe kudi mai yawan gaske don jigilar mai zuwa cikin kasar. Bamban da haka, ya kan sayar da mai a kasuwannin wurin".

A karshe dai, Mr. Fu Chengyu ya jaddada, cewa a da, an yi kuskuren cewa, wai duk inda kamfanonin kasar Sin suke haka mai a can, za su yi jigilar shi zuwa cikin kasar. A hakika dai, ba haka take yi ba. Lallai ra'ayin da aka fito na cewa wai kasar Sin tana habaka yunkurin samun makamashi a ketare ya kasance tamkar gadar zare ce zalla! (Sani Wang)