Bisa sabon rahoto da hukumar kula da harkokin teku ta kasar Sin ta bayar a kwanakin baya, an ce, jimlar kudi da kasar Sin ta samu daga wajen albarkatun teku ta wuce kudin Sin Renminbi Yuan biliyan 1,000 a farkon rabin shekarar nan.
]A cikin rahoto da wannan hukumar ta bayar a kan yadda ake gudanar da harkokin tattalin arzikin tekuna na kasar Sin a farkon rabin shekarar nan, an ce, jimlar kudin da kasar Sin ta samu daga wajen albakatun teku ya kai kudin Sin Yuan biliyan 1134.2 a farkon rabin shekarar nan, wato ke nan ta dauki kashi sama da 10 cikin dari na jimlar kudi da kasar ta samu daga wajen samar da kayayyaki.
Wani jami'in hukumar ya bayyana cewa, ya kasance da gibi a tsakanin kasar Sin da kasashe masu sukuni a fannin bunkasa harkokin tattalin arzikin tekuna. Nan da shekaru 5 ko 10 mazu zuwa, an kyautata zaton cewa, jimlar kudi da kasar Sin za ta samu daga wajen tattalin arzikin tekuna za ta dauki kashi 20 cikin dari na jimlar kudi da take samu daga wajen samar da kayayyaki. (Halilu)
|