Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-10 15:27:07    
Wasu labaru game da kabilun kasar Sin

cri

A cikin shirinmu na yau, da farko dai ga wasu labaru game da kabilun kasar Sin.

Labarin farko shi ne kasar Sin za ta kara yin kokarin wajen tabbatar da moriyar kananan kabilu a fannin tattalin arziki da siyasa

Kwanan baya, Hui Liangyu, mataimakin firayin ministan kasar Sin ya bayyana a birnin Hohhot, hedkwatar jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta, cewar kasar Sin za ta kara aiwatar da Dokar da ta amincewa 'yan kananan kabilu su aiwatar da harkokinsu da kansu a yankunansu da sauran dokokin da abin ya shafa domin raya da tabbatar da moriya da ikon kananan kabilu a fannonin tattalin arziki da siyasa da al'adu.

Hui Liangyu ya fadi haka ne a gun taron nuna yabo ga wadanda suke kokarin hada kan al'ummomi daban-daban a jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta da aka shirya a kwanan baya.

Ya kara da cewa, a nan gaba, za a ilmantar da matasa da yara na kabilu daban-daban cewa, "kabilar Han ba za ta iya zama da kanta ba idan babu sauran kabilu, sauran kabilu daban-daban ma ba za su iya zama da kansu ba idan babu kabilar Han. Kananan kabilu daban-dabam ma suna dogara da juna". Kuma za a kara mai da hankali wajen raya kauyuka da unguwannin da ke cike da jituwa da hadin guiwa. Bugu da kari kuma, za a yi namijin kokari wajen daidaita matsaloli da wahaloli masu tsanani da suke kasancewa a gaban jama'ar kabilu daband-aban kai tsaye. Sabo da haka, za a iya mayar da sakamakon da aka samu daga wajen bunkasuwa a fannin kokarin kyautatuwar rayuwar jama'a.

Wani labari daban shi ne makiyaya dubu 30 na kabilar Tibet sun shiga garuruwa daga tushen manyan koguna 3

Ya zuwa karshen watan Yuni na shekarar da muke ciki, yawan makiyaya na kabilar Tibet wadanda suke zama a wuraren tushen manyan koguna 3 kuma suka shiga garuruwa da birane sun riga sun kai dubu 30. Bayan shigarsu cikin garuruwa, sun samu wuraren kwana da kudin tallafi da wasu manufofin ba da gatanci da gwamnatin kasar Sin ta samar musu.

Yankin tsaron tushen manyan koguna 3 mafi tsawo, wato kogin Huang da na Yangtse da Lancangjiang, yana cikin tudun Qinghai-Tibet. A cikin shekaru da yawa da suka wuce, aikace-aikacen da dan Adam ke yi da dalilan halittu sun haifar da illa tare da lalata yanayin daukar sauti na wannan yanki.

Tun daga shekarar 2005, gwamnatin kasar Sin ta soma aiwatar da ayyukan kiyaye wannan yankin tushen manyan koguna 3. Sabo da haka, dimbin makiyaya wadanda suka dade suna zama a cikin yankin sun fara kaura zuwa garuruwa domin tabbatar da ingancin filin ciyayi na yankin tushen manyan koguna 3. Wani jami'in ofishin gudanar da ayyukan kiyaye tushen manyan koguna 3 na lardin Qinghai ya bayyana cewa, yanzu, yawan mutanen da suke son kaurawa yana ta karuwa. An yi hasashen cewa, ya zuwa shekarar 2010, yawan makiyayan kabilar Tibet da za su shiga garuruwa zai kai fiye da dubu dari 1.

Labarin karshe na yau shi ne ana bunkasa adabin Tibet kamar yadda ake fata

A cikin 'yan shekarun da suka wuce, adabi da fasahohin zane-zane na jihar Tibet suna samun cigaba kamar yadda ake fata. Adabin da ke bayyana hakikanan zaman rayuwar jama'a da fim da adabin da ake rubuta da kalmomin kabilar Tibet sun samu sakamakon da za a iya yin alfahari da su.

Bisa kididdigar da aka yi, tun daga shekarar 1999, yawan litattafan adabi , ciki har da tatsuniyoyi da rububattun wakoki da rubuce-rubucen zube da tatsuniyoyin yara da marubutan kabilu daban-daban na jihar Tibet mai cin gashin kanta suka rubuta ya kai fiye da dari daya. Wasu daga cikinsu sun samu lambobin yabo iri daba-daban a kasar. (Sanusi Chen)