Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-10 10:24:27    
Mr.Hu Jintao ya dawo birnin Beijing bayan ya gama ziyararsa

cri
A ran 10 ga wata da safe shugaban kasar Sin Mr.Hu Jintao ya komo kasar Sin, bayan ya yi ziyarar aiki a kasar Australia da kuma halartar kwarya-kwaryar taro na karo 15 na shugabannin kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta Asiya da tekun Pacific wato taron koli na kungiyar APEC.

Shekarar bana shekara ce ta cikon shekaru 35 da Sin da Australia suka kulla huldar diplomasiya a tsakaninsu, ziyarar da Mr.Hu Jintao ya yi a wannan gami a Australia ziyarar aiki ce ta karo daban da ya yi a wannan kasar bayan shekaru 4 da suka wuce. A gun taron koli na kungiyar APEC, Mr.Hu Jintao ya bayar da matsayin da kasar Sin take dauka kan batun sauye-sauyen yanayi da neman bunkasa kungiyar APEC da sauran batutuwa.

Sakataren sakatariya na kwamitin tsakiya na J.K.S Mr.Wang Gang da ministan harkokin waje na kasar Sin Mr.Yang Jiechi da darektan kwamitin yin gyare-gyare da raya kasar Sin Mr.Ma Kai da ministan kasuwanci na kasar Sin Mr.Bo Xilai da sauransu wadanda ke rufawa Mr.Hu Jintao, bayan ziyarar sun iso kasar Sin tare da Mr.Hu Jintao.(Abubakar)